"Da Na Kowa Ne": Uwa Ta Fadi Yadda Lakcara Ya Kore Ta a Aji Don Kukan Jinjiranta, Bidiyon Ya Janyo Cece-Kuce

"Da Na Kowa Ne": Uwa Ta Fadi Yadda Lakcara Ya Kore Ta a Aji Don Kukan Jinjiranta, Bidiyon Ya Janyo Cece-Kuce

  • Wata mata ta wallafa wani faifan bidiyo inda ta ke bayyana yadda malami ya koreta a cikin aji da ‘yarta
  • Malimin ya kore ta ne saboda ‘yarta ta yi kuka wadda hakan ya fusata matar da cewa ya ci mutuncinta
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu yayin da kusan dukkansu suke ganin malamin bai kyauta ba

Wata mata a Najeriya ta bayyana yadda wani malaminsu ya fatattaketa a aji saboda kukan jaririyarta.

Matar mai suna @sheisteemah a wani faifan bidiyo a TikTok ta halarci aji don daukar darasi a makarantar tare da ‘yarta karama wadda ko tafiya ba ta iya ba.

Uwa/jinjira/lackara
Lakcara ya fatattaki uwa da yarta daga ajinsa. Hoto: @sheisteemah
Asali: TikTok

A lokacin da malamin ke koyarwa, sai ‘yar ta kwarara ihu wanda hakan ya fusata lakcaran nasu inda shi kuma bai yi wata-wata ba dukkansu ya kore su daga ajin.

Kara karanta wannan

Matan Zamani: Mata Ta Sace ’Yar Cikinta, Ta Nemi Kudin Fansa N3m Daga Wurin Mjinta

Matar ta nuna bacin ranta yadda malamin ya ci mutuncincu a cikin bidiyon, amma sai ta ce ba laifinsa ba ne laifin yarinyar ne ita ta jawo mata cin mutunci.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matar ta yi rubutu kamar haka:

“Yar ka za ta jawo maka cin mutunci saboda yin kuka a aji, malamin kuma ya kora mu waje gaba daya”.

Ga bidiyon a kasa:

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu

@omolara233:

“Karki damu. ‘Yarki za ta kawo miki alkairai.”

@slimzzy826:

“Malamin ba shi da yara ko, watakila ‘yar ta tsane shi.”

@mokebaby:

“Haka su ke yi kaman ba su da yara a gida, ‘yar ki alkairi ce.”

hunsuestheryemayi:

“Kar ki damu haka suke kaman ba su haifi ‘ya’ya ba, yaran su na gida tare da mamansu ita kadai.”

@leachiey:

“Hhhhh don Allah ki yafe mata. Yanda ba ta son kallon abin daukar hoton kaman ta san laifin da ta yi.”

Kara karanta wannan

"Soyayyar Nesa Akwai Wuya": Matashi Ya Sharbi Kuka Yayin Da Kyakkyawar Budurwarsa Baturiya Zata Koma Kasarsu

@pweetyej:

“Wani malaminmu duk lokacin da wani jariri ke kuka, zai dauke shi kafin wani lokaci jaririn ya yi bacci.”

estherlovth:

“Me ya sa kuke yi masa kallon bai kyauta ba, kukan wasu yaran ya na dauke hankalin malamin da kuma dalibai.”

UwaTa Ɗaure Ƙafar Ɗanta a Kujera Saboda Ɓarnar Da Yake Yi Mata a Shago

A wani labarin, wata uwa ta daure kafar danta a jikin kujerar shago saboda tsananin rikicin yaron, wanda kullum sai ya jawo mata asara.

A cikin wani faifan bidiyo, an gano matan cikin fushi tana nuna yadda ke mata barna, da kuma yadda ya yi kaca-kaca da shagon cikin kankanin lokaci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel