Katsina Sun Shirya Addu'ar Tunawa da Tsohon Shugaban Kasa Yar'Adua
- Katsinawa da masu ruwa da tsakin PDP a jihar Katsina sun ƙara yi wa tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'Adua addu'ar Allah ya jikansa
- A ranar Jumu'a 5 ga watan Mayu, 2023, Umaru Musa Yar'adu'a ya cika shekara 13 da rasuwa
- Masu shirya taron sun ce mutane ba zasu manta da Yar'adua ba a Najeriya saboda kyawawan halayensa da nagarta
Katsina - Wasu yan jihar Katsina a ranar Jumu'a sun haɗu da masu ruwa da tsakin jam'iyyar PDP reshen jihar, sun gudanar Addu'o'in neman rahama ga Marigayi Umaru Musa 'Yar'Adua.
Channels tv ta rahoto cewa taron Addu'o'in wani bangare ne na abubuwan da aka shirya domin tunawa da tsohon shugban ƙasan, wanda ya cika shekaru 13 da rasuwa.
Gamayyar ƙungiyoyin magoya bayan PDP ne suka shirya taron Addu'o'in wanda ya gudana a hedkwatar jam'iyyar da ke cikin birnin Katsina.
Yar'Adua shugaba ne abin koyi a Najeriya - PDP
Shugaban kwamitin rikon kwarya na PDP a Katsina, Abdurrahman Usman, Dakta Abdurrahman Usman, wanda Lawal Rufa’i Safana, ya wakilta ya ayyana marigayi da abin kwatance a siyasa da shugabanci.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Ba abu ne mai sauki a samu wanda ya haɗa tunaninsa da nagartarsa. Muna fatan wataran Allah ya kawo mana wanda zai kwatanta halayensa, zamu yi maraba da hakan."
"Muna da yaƙinin yan Najeriya zasu ci gaba da tuna kyawawan ayyukan marigayi tsohon shugaban masa Yar'adua a kowane fannin shugabancin ƙasa da ci gaban ƙasa."
A nasa jawabin, wanda ya shirya taron Addu'o'in, Malam Hamza Jibia, ya ce wannan ne karo na biyar da suka shirya taron addu'a da nufin tuna ayyukan tsohon shugaban Najeriya.
A kalamansa, Malam Hamza ya ce:
"Wannan karon bamu shirya lakca ba wacce ake faɗin kyawawan abubuwa game da mamacin musamman halayensa masu kyau da ya nuna lokacin da ya yi gwamna da shugaban ƙasa."
Shiri Ya Kwabe: Jigon Jam'iyya Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe
Legit.ng Hausa ta zanta da wasu al'ummar jihar Katsina kan wannan rashi, inda da yawansu suka ce Marigayi shugabane abin misali a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.
Abdul-Hafiz Tukur, haifaffen jihar Katsina, ya ce ba zasu taba mantawa da ayyukan Umaru Musa ba a Katsina domin har yanzun a ido na ganin wasu ayyuan da ya yi.
"Bawan Allah nagari kenan, Marigayi Yar'adua ya yi abubuwan da ba zamu manta ba, ba abinda zance sai Allah ya jaddada rahama a gare shi," inji shi.
Haka zalika wani jigon PDP, Idris Umar, ya ce tarihin Najeriya ba zai kammalu ba sai an haɗa da marigayi tsohon shugaban ƙasa, Umaru Musa Yar'Adu.
Ya ce:
"Ba'a taba adalin shugaba a Najeriya kamar Yar'Adua ba tun da aka dawo mulkin Demukradiyya a 1999, kowa ya san haka kuma duk wanda ka tambaya ba zai faɗi abu mara kyau a kansa, Allah ya jikansa."
Tinubu, Atiku Ko Obi? Tsohon Shugaban Kasa Ya Roki Alfarma 1 Wurin Yan Najeriya Kan Shari'ar Zaben 2023
Shugaba Buhari Ya Sabunta Wa'adin Shugabancin Yan Majalisar Amintattu Na NPTF
A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Kara Yin Muhimman Nade-Nade Saura Kwana 24 Ya Sauka Mulki
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da sabunta naɗin mambobin majalisar amintattuna na asusun kula da walwalar yan sandan Najeriya.
Asali: Legit.ng