Hotunan Wata Zankadediyar Budurwa Bayan Ta Yi Aure Ya Girgiza Intanet

Hotunan Wata Zankadediyar Budurwa Bayan Ta Yi Aure Ya Girgiza Intanet

  • Wata mata a Najeriya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ta wallafa Hotunanta bayan ta shiga rayuwar aure
  • Matar ta saki Hotunan kafin ta shiga daga ciki, lokacin aure da kuma bayan ta sha fama da rayuwar aure
  • Da yawan 'yan Najeriya masu amfani da soshiyal midiya sun nuna kaɗuwa da rashin aminta da yadda matar ta koma, wasu sun faɗi inda aka samu matsala

Wata mata 'yar Najeriya mai suna, Uche Annabel, ta girgiza kafafen sada zumunta bayan ta wallafa Hotunan sauyin da surar jikinta ta yi bayan ta yi aure.

Uche ta shiga gasar soshiyal midiya, wanda mutane ke tura Hotunan kamannin su gabanin aure da kuma bayan sun shiga daga ciki.

Uche Annabel.
Hotunan Wata Zankadediyar Budurwa Bayan Ta Yi Aure Ya Girgiza Intanet Hoto: Uche Annabel
Asali: Getty Images

Yayin da ta wallafa Hotunan a dandalin sada zumuntar Facebook, matar ta bayyana cewa babu abinda zata iya faɗa.

Kara karanta wannan

“Turo Mun N400k Ko Na Rabu Da Kai”: Matashiya Ta Yi Barazana Ga Saurayinta, Hoton Hirarsu Ya Bayyana

Ta rubuta cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ku duba ni gabanin na yi aure, lokacin ina da aure da kuma bayan rayuwar aure. Allah, ba ni da abinda zan faɗa."

Hotunan sun nuna matar zankadediya ce son kowa kin wanda ya rasa gabanin ta yi aure da bayan auren ya mutu, amma hotunan lokacin da take da aure ya girgiza mutane.

Sai dai babu tabbacin ko matar na da aure a yanzu kuma ba ta fayyace ba a rubutun da ta wallafa.

Martanin mutane a soshiyal midiya

Cynthia Jacob ta ce:

"Yar uwa ya kamata kisani cewa a lokacin aurenki shi ne lokacin da wata ke budurwa, yadda kike bayan aure shi ne wata ke cikin aure. Saboda haka ki rabu da mu da wannan rubutun, aure da daɗi mun gode Allah."

Momoh Loveth ya ce:

"Koma me kika sa a ranki, wannan ɗacin labarin naki ba zai sa ni da Rachael James mu ji tsoron aure ba. Kawai baki sa'a bane, mu kuma da kafar dama zamu shiga."

Kara karanta wannan

“Ba Zan Iya Bacci Ni Kadai Ba”: Uwa Ta Bude Kofar Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta, Mutane Sun Bata Shawara

“Baka Ji Kunya Ba?” Matashiya Ta Caccaki Saurayinta Kan Tura Mata N70k Maimakon N400k

A wani labarin kuma Soyayyar wata budurwa ta fara tangal-tangal bayan ta roki Saurayinta kuɗi N400k.

Wata Budurwa ta fusata da kuɗin da saurayinta ya turo mata, Ta Gaya masa ya turo adaɗin da ta nema ku su rabu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel