“Za Ta Daina”: Wara Uwa Ta Bude Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta

“Za Ta Daina”: Wara Uwa Ta Bude Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta

  • Wata uwa da ke cike da damuwa ta yi wani bidiyo da ke nuna diyarta kwance a kan gadon kaninta da daddare saboda tana jin tsoro
  • Matar wacce ta yi korafin cewa a kodayaushe yayar na satar jiki ta kwanta kan gadon kaninta ta nemi jin shawarwarin mutane kan yadda za ta yi maganin abun
  • Mutane da dama da suka bata shawara sun bayyana cewa yarinyar za ta daina tsoron nan gaba yayin da wasu suka ba da shawarwari irin na iyaye

Wata uwar yara uku (@queen_already1) wacce ke yawan sanya bidiyoyin ban dariya game da iyalinta a TikTok, ta dauki bidiyon diyarta mace kan gadon kaninta.

Matar ta ce a kulla yaumin yarinyar na shigewa dakin dan uwan nata don yi bacci da daddare saboda tana tsoro. Matar ta bukaci mutane da su bata shawara kan yadda za ta magance lamarin.

Kara karanta wannan

Wata Budurwa Ta Ce Bata Bukatar Saurayi, Ta Fallasa Sakonnin Da Yayanta Ya Aike Mata

Uwa da diyarta budurwa
“Za Ta Daina”: Wara Uwa Ta Bude Daki, Ta Gano Diyarta Kwance a Gadon Kaninta Hoto: @queen_already1
Asali: TikTok

Uwa da ke cike da damuwa ta nemi shawara

Mutane da dama da suka kalli bidiyon matar sun garzaya sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu. Akwai yan TikTok da suka ce kada ta damu kuma cewa yarinyar za ta daina.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A lokacin da wnai mutum ya yi kokarin tunani mara kyau kan lamarin, matar ta hayayyako masa, cewa shekarun yaron shida a duniya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

user9781920561582 ya yi martani:

"Watakila akwai wani abu a ciki dan Allah ki dauki abun da muhimmanci koda kuwa zai kai ki ga dasa kamara a dakinta da gano dalili."

Skyprince Multiple ya ce:

"Kawai ki kyale ta, tana jin dadin kasancewa tare da kaninta kin ji...Ina ma ace ina da yar'uwa kamar haka."

survive ta ce:

"Babu wani aibu ba wani abu bane."

Kara karanta wannan

Bani da ko saurayi: Budurwa ta ce tallan gwanjo na kai mata, ta sayi motar N36m

Larry - gold ta ce:

"Za ta daina ne."

Hleighta ce:

"Dan ki na iya kwanciya a wani wurin daban sannan idan ta zo kwanciya a gadon kaninta sai ta ga baya nan."

Michaelmas ya ce:

"Ni ina ganin tana kare kannenta ne."

user2128137823077 ta ce:

"Ni kenan bana iya bacci ni kadai. ina tsoron mugayen mafarki ina bacci tare da mahaifiyata shekaruna 303."

Matashi ya zauce bayan ya gano mahaifinsu daya da budurwar da ke dauke da cikinsa

A wani labari na daban, wani matashi ya samu lalurar tabin hankali bayan ya gano cewa mahaifinsu daya da budurwarsa wacce ke dauke da cikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel