Tinubu Bai Bi Ta Gwamnonin APC Ba, Ya Ce Gwamnan PDP Wike Ne Ya Taimake Shi Ya Ci Zaben 2023
- Bola Tinubu ya ce gwamna Wike ya taimake shi wajen lashe zaben shugaban kasa na wannan shekarar da aka yi
- Ya bayyana yadda gwamnan ya bashi gudunmawa wajen samun nasara, duk da kuwa ba a jam’iyya daya suke ba
- Jam’iyyar APC ta nesanta kanta daga alakar Tinubu da Wike, ta kuma yi watsi da ziyarar da zababben shugaban kasar ya kai Ribas
Jihar Ribas - Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya ya ce, ba dan goyon bayan da ya samu daga gwamnan PDP Nyesom Wike na Ribas ba, da ya dungura a zaben shugaban kasa.
A ranar 1 ga watan Maris ne aka alanta Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya, inda ya samu kuri’u 8,794,726 a jihohin kasar, TheCable ta ruwaito.
Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu na zaben, inda ya samu kuri’u 6,984,520 yayin da Peter Obi na jam’iyyar Labour ya zo na uku da kuri’u 6,101,533.
Obi da Atiku sun fusata da sakamakon zabe, inda suka dunguma zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon da hukumar zabe ta INEC ta fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar Tinubu da Wike bayan zaben shugaban kasa
A yayin ziyarar da ya kai jihar Ribas, Tinubu ya bi gwamnan jihar zuwa kaddamar da aikin gadar sama ta Raumuokwuta/Rumuola da aka gina a birnin Fatakwal na jihar a yau Laraba 3 Mayu, 2023.
A cewar Tinubu a wurin taron kaddamar da aikin, taimakon da ya samu a wurin Wike ya yi tasiri matuka wajen nasararsa a zaben shugaban kasa na bana, rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, akwai ‘yar tsama tsakanin gwamnan na PDP da kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku tun gabanin zaben shugaban kasa na bana.
Hakazalika, jam’iyyar APC ta bayyana nesanta kanta da alakar Tinubu da gwamnan na PDP, inda ta nemi kada ya kai ziyara jihar ta Ribas a yau.
APC ta nesanta kanta da ziyarar Tinubu a jihar Ribas
A wani labarin, kunji yadda gwamna Wike ya gayyato Tinubu domin shafe kwanaki biyu a jiharsa don kaddamar da wasu manyan ayyukan da ya yi a Ribas.
Tuni jam’iyyar APC ta bayyana nesanta kanta da wannan ziyarar, inda ta bayyana rashin jin dadi da alakar Tinubu da Wike.
Gwamna Wike da Tinubu, zababben shugaban kasa dai na dasawa a wannan lokacin, ana zargin Wike da cin dunduniyar jam’iyyarsa.
Asali: Legit.ng