Bincike: Yaron Tinubu Ya Saye Gidan Landan da Ake Zargin na Sata ne a Naira Biliyan 5

Bincike: Yaron Tinubu Ya Saye Gidan Landan da Ake Zargin na Sata ne a Naira Biliyan 5

  • Ana zargin kamfanin Aranda Overseas Corp ya saye wani gida da Mista Kolawole Aluko ya mallaka
  • Yaron shugaban Najeriya mai jiran gado, Oluseyi Tinubu shi ne yake da kamfanin da ya lale $11m
  • EFCC ta na zargin Aluko ya ba Diezani Alison-Madueke cin hancin kudi domin samun kwangiloli

UK - Wani kamfani da Seyi Tinubu ya mallaka, ya kashe $11m wajen sayen katafaren gida da gwamnatin tarayya ta ke binciken mai shi a kasar Birtaniya.

Wani bincike na Bloomberg ya nuna yaron zababben shugaban kasar ya saye wannan gida a Landan da ake zargi da dukiyar sata aka mallake shi.

Babu abin da yake nuna akwai hannun zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu wajen cinikin a 2017. Seyi yana cikin ‘ya ‘yan shugaban mai jiran gado.

A Agustan 2021, Shugaba Muhammadu Buhari ya taka da kafafunsa, ya ziyarci Bola Tinubu a gidan a lokacin da gwamnatinsa ke yaki da rashin gaskiya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Fadawa Bola Tinubu Alfarmar da Yake Nema a Wajen Gwamnatinsa

Gidan kusan Naira Biliyan 5

Jaridar kasar wajen ta ce akwai alamar tambaya game da dukiyar zababben shugaban na Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oluseyi Tinubu mai shekara 37 a Duniya shi ne babban mai hannun jari a kamfanin Aranda Overseas Corp wanda ya biya £9m ($10.8m), ya saye gidan.

Seyi Tinubu
Seyi Tinubu da mahaifinsa Hoto: naijablog.ng
Asali: UGC

Kamar yadda bincike ya nuna, an tura kudin katafaren gidan da ke yankin St. John’s Wood a Arewacin birnin Landan a kasar Ingila ta bankin Deutsche Bank.

A gidan akwai wuraren ajiye motoci takwas, lambu biyu da kofa mai aiki da lantarki da wurin motsa jiki, wata jaridar Ingila ta ce tsawon gidan ya kai kafa 14, 000.

Da aka tuntubi Oluwaseyi Tinubu da Mai magana da yawun bakin mahaifinsa ta imel, lambar waya da sakonni domin jin ta bakinsu, ba su yarda sun ce uffan ba.

Daily Trust ta ce Lauyan da shi ne dillalin kamfanin da aka yi cinikin shi ya ki yarda ya yi magana.

Kara karanta wannan

Binani ce ta ci zabe: Hudu Ari ya fasa kwai, ya ce manya a INEC sun karbi cin hanci daga Fintiri

Wanene ya mallaki gidan?

Maganar da ake yi, a halin yanzu gwamnatin tarayya ta na binciken wanda ya saida wannan gida - Kolawole Aluko, ana zarginsa a cikin badakalar Dala $1.5bn.

Tun farkon hawan Buhari ake binciken tsohuwar Minista, Diezani Alison-Madueke a kan zarginta da karbar rashawa a hannun Mista Aluko da Olajide Omokore.

Binciken Diezani Alison-Madueke

A kwanakin baya an samu rahoto cewa EFCC ta shirya yin gwanjo da kadarorin wasu ‘yan siyasa da ‘yan kasuwan da aka samu da laifin taba baitul-mali.

Lamarin ya shafi Diezani Alison-Madueke, kadarorin da za a sa a kasuwa su na garuruwan Legas, Ribas, Abuja, Anambra, Gombe, Ebonyi da kuma Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng