Da duminsa: Babban basarake a jihar Sokoto ya rasu

Da duminsa: Babban basarake a jihar Sokoto ya rasu

- Allah ya yi wa Alhaji Sa'ad Mainasara Dahiru, hakimin garin Tambuwal da ke jihar Sokoto, rasuwa

- Basaraken ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da ya yi a garin Abuja a ranar Alhamis

- An yi jana'izarsa tare da birnesa kamar yadda addinin Musuluncin ya tanadar a garin Tambuwal a ranar Juma'a

A yau ne aka birne hakimin Tambuwal a jihar Sokoto, Alhaji Sa'ad Mainasara Dahiru.

Basaraken mai shekaru 58 a duniya ya rasu ne a ranar Alhamis a garin Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

An birne shi a garinsu na Tambuwal da ke jihar Sokoto.

A wata takarda da ya fitar a ranar Juma'a, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya yi addu'ar gafarar Allah ga mamacin, tare da dauriyar jure rashin da ga iyalansa.

A wani bangare kuwa, titin Sokoto zuwa Tambuwal ya cika da jama'a masu kaiwa da kawowa tun a safiyar ranar Juma'a.

Masu zuwa gaisuwa, 'yan uwa da abokan arziki ne da suka hada da manyan jami'an gwamnati, 'yan majalisu da 'yan siyasa ke ta tururuwar zuwa gaisuwar ta'aziyyar basaraken.

An yi jana'izarsa a garin Tambuwal tare da Gwamna Tambuwal, manyan jami'an gwamnati da 'yan siyasa.

Da duminsa: Babban basarake a jihar Sokoto ya rasu
Da duminsa: Babban basarake a jihar Sokoto ya rasu. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Zargin gwamnan arewa da Boko Haram: Wurin 'yan kasuwar kauye na samu labari - Mailafiya

A wani labari na daban, An birne gogaggen dan siyasa kuma makusanci ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Malam Isma'ila Isa Funtua a Abuja. Funtua, wanda siriki ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma babban abokinsa, ya rasu a Abuja a ranar Litinin.

An birnesa a makabartar Gudu, bayan sallatar gawarsa da aka yi a babban masallacin Shehu Shagari da ke Area 1, Garki, a garin Abuja.

Wasu daga cikin jiga-jigan da suka samu halartar jana'izar sun hada da Mamman Daura, dan uwa kuma makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari Akwai Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe; Nduka Obaigbena, shugaban gidan jaridar THISDAY da ARISE TV; da Sam Nda-Isaiah, mwallafin jaridar Leadership.

Gwamnan jihar Yobe tare da Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, duk sun halarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: