Tsohon Minista ya Jero Tarihi 20 da Buhari, APC, Tinubu da Obi Suka Bari a Zaben 2023
Abuja - A yayin da ake murnar dawowar Bola Ahmed Tinubu, Femi Fani-Kayode ya zakulo tarihin da yake ganin an kafa a 2023.
A zaben shugaban kasa na bana ne aka samu Ibo ya doke Bayarabe a Jihar Legas.
Daga cikin abubuwan da za su shiga littafin tarihin Najeriya shi ne mutumin Arewa zai sauka daga kan karagar mulki salin-alin.
Ga tarihin da aka kafa:
1. Muhammadu Buhari zama mutumin Arewa da ya fi kowa dadewa a kan kujerar shugaban kasa a mulkin farar hula.
2. Shugaba Muhammadu Buhari zai zama ‘Dan Arewa na asali da ya karasa mulki ba tare da an masa juyin mulki ko ya mutu ba.
3. Bola Ahmed Tinubu zai zama Musulmin farko daga Kudancin Najeriya da zai zama shugaban kasa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
4. A karon farko, an samu Babarbaren da zai zama Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
5. Ba a taba yin lokacin da za a rantsar da Musulmi da Musulmi a mulkin farar hula ba sai a bana.
6. Ibo ya yi nasara a zaben shugaban kasa a Legas, Nasarawa da Abuja, ya samu 94% na kuri’un Kudu maso gabas.
7. Wannan ne karon farko da Atiku Abubakar bai iya yin nasara a jiha ko daya daga Arewa maso tsakiya ba.
8. A 2023 ne aka samu mafi yawan jagororin Arewa sun tashi tsaye, sun ce dole mulki ya koma Kudu.
9. A zaben nan ne coci ta fito karara ta goyi bayan ‘dan takara, Peter Obi wanda a karshe bai ci ba.
10. Bola Ahmed Tinubu ya gamu da suka da makarkashiya iri-iri, amma ya samu tikiti, ya lashe zabe.
11. Sai a zaben wannan karo ne aka taba samun hadin-kai sosai tsakanin Arewa da Yarbawa a siyasa.
12. Baro-baro aka ji ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa (Yusuf Datti Baba-Ahmed) yana yi wa Shugaban kasa, INEC da kotu barazana.
13. Har ila yau, a zaben 2023 ne abokin gamayya ya fashe da kuka a gidan talabijin (Yusuf Datti Baba-Ahmed) saboda an taba mahaifinsa).
14. Peter Obi ya hada zaben shugaban kasa da yakin addini, ya yi kira ga fastoci su taimaka masa a cocinsu.
15. Bayan zaben wannan karo ne aka samu mutumin da ya hana jirgin sama tashi saboda ‘dan takaransa bai yi nasara ba.
16. An lashe zabe ba tare da an tsaida Bafullatani ko kirista a jam’iyyar da tayi galaba ba, abin da ba a taba gani ba.
17. Abin ban mamaki, ‘Dan takaran PDP (Atiku Abubakar) bai yi nasara a Ribas ba, bai samu ko da 25% ba.
18. Za a samu Fasto, Sanata kuma tsohuwar Uwargidar Legas a matsayin Uwargidar shugaban kasa.
19. Shugaban kasa da Shugaba mai jiran gado sun yi bikin sallah tare, dukkaninsu Musulmai ne.
20. Musulmi zai mika mulki ga Musulmi a ranar 29 ga watan Mayun 2023, hakan bai taba faruwa ba.
Jirgin Nigeria Air Limited
Nigeria Air Limited zai fara aiki kafin karshen wa’adin gwamnatin nan, Ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika yace bai janye kalamansa ba.
Hadi Sirika ya fadawa ‘yan jarida a Abuja sun tanadi abubuwan da ake bukata tun daga jiragen saman, ofisoshi, ma’aikata da abubuwan da za a nema.
Asali: Legit.ng