Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Ministan Kwadago Gwadabe Ya Kwanta Dama

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Ministan Kwadago Gwadabe Ya Kwanta Dama

  • Yanzu muke samun labarin yadda wani tsohon ministan Najeriya, Musa Gwadabe ya kwanta dama bayan karamar jinya
  • Alhaji Gwadabe ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 11 da kuma tarin jikokin da ba a bayyana adadin yawasu ba
  • Hakazalika, a yau ne za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a yau Laraba 26 Afirilu, 2023, kamar yadda rahoto ya fada

Jihar Kano - Tsohon minsitan kwadago kuma jigon jama’iyyar PDP, Musa Gwadabe ya kwanta dama, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Allah ya yiwa Gwadabe rasuwa ne a ranar Laraba 26 Afirilu, 2023 yana da shekaru 87 a duniya bayan wata jinya da ya yi a asibitin jihar Kano, inji dangin kusa.

Gwadabe ya kasance tsohon sakataren gidan gwamnan jihar Kano a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Ankarar da Kotu a Kan Babbar ‘Hujjar’ da ke Nuna Magudin Bola Tinubu

Daily Trust ta ruwaito cewa, za a yi jana’izarsa da misalin karfe 2 na rana a yau Laraba a gidansa da ke Ado Madaka a jihar ta Kano.

Allah ya yiwa Gwadabe rasuwa
Alhaji Musa Gwadabe na jihar Kano kenan | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 11 da kuma tarin jikokin da majiya bata bayyana ba.

Daga cikin ‘ya’yansa, akwai Alhaji Nazifi Musa Gwadabe, wani fitaccen dan kwangila a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Yadda ya rike makamai

Alhaji Gwadabe ya yi minista ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2003.

Ya kuma rike kujerar sakataren gwamnati a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Sabo Bakin-Zuwo.

Ya zuwa rasuwarsa, shine shugaban kwamitin asusun horarwar masana’antu na ITF, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Shugaban 3SC, Baba Lankondaro, Ya Mutu

Kara karanta wannan

Malamin Jami'ar Najeriya A Jihar Arewa Ya Rasu Yana Cikin Barci

A wani labarin, kunji yadda Najeriya har ila yau ta yi babban rashin wani tsohin jigo kuma mai fada aji a kasar a watan Afrilu.

Allah ya yiwa tsohon shugaban 3SC, Baba Landondaro rasuwa, kamar yadda rahotanni na kusa da dangi ke bayyanawa.

Rahoton da muka samo ya bayyana kadan daga tarihinsa da kuma irin tasirin ayyukansa ga yadda Najeriya ke ciki a baya da kuma a yanzu.

A cewar majiya, Baba ya rasu ne yana da shekaru 111 a duniya, Allah ya bashi aron lokaci mai tsawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.