Gwamnatin Tarayya ta Tsokano Fada, An yi wa Ma’aikata Karin Albashi, An Ware jami’o’i

Gwamnatin Tarayya ta Tsokano Fada, An yi wa Ma’aikata Karin Albashi, An Ware jami’o’i

  • Ma’aikatan cibiyoyi, ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya sun samu karin kudi a albashi
  • Bayan karin 40%, nan take aka biya bashin wannan karin na watannin shekarar nan da suka gabata
  • Amma malaman jami’an gwamnati sun ce duk abubuwan da ke faruwa, sai dai su ji labari a makwabta

Abuja - Akwai alamu da ke nuna kungiyoyin ma’aikatan jami’a za su sa wando daya da gwamnatin tarayya bayan an ware su a karin albashi da aka yi.

Rahoton da aka samu a Vanguard ya nuna babu ma’aikatan jami’o’in gwamnati a karin 40% da ma’aikatan gwamnatin tarayya suka samu a albashinsu.

Baya ga karin albashin da aka samu a watan Afrilu, an biya ma’aikata bashin karin da aka yi.

Ma’aikatan jami’o’i sun yi tir da yadda aka maida su saniyar ware yayin da masu aiki a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati suke gwangwajewa.

Kara karanta wannan

An Bar ‘Yan Najeriya Cirko-Cirko, Sudan ta Hana Mutanen Afrika Ficewa a Tsakiyar Yaki

Za a hada da ma'aikatan jami'a

Amma gwamnatin tarayya ta fito ta nuna cewa babu wani abin tada jijiyoyin wuya a game da lamarin domin karin zai shafi ma’aikatan da ke jami’o'i.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan kwadago, Chris Ngige ya nuna ana jiran cin ma matsaya da kungiyar ASUU a kan batun yarjejeniyar CBA da tsarin albashi ne kafin a biya su.

Shugaban kasa da SGF
Shugaban kasa da Saataren Gwamnatin Tarayya Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Rahoton ya ce sai an kammala wannan zama tsakanin wakilan ASUU da ma’aikatar ilmi ta kasa, sannan za a kai maganar zuwa hukumar yanka albashi.

Ba a neman zaman lafiya - SSANU

Shugaban kungiyar SSANU na kasa, Kwamred Mohammed Ibrahim ya ce hana ma’aikatan jami’a karin kudin da aka yi, yunkurin kawo rikici ne kurum.

Kwamred Ibrahim ya shaidawa jaridar cewa har yau ba a biya su alawus din N50bn da gwamnatin tarayya ta ke ikirarin ta sa a cikin kasafin kudin 2023 ba.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya, Allah Ya Yi Wa Fitaccen Alƙalin Babbar Kotun Arewa Rasuwa

Malaman jami'a sun yi Allah-wadai

Legit.ng Hausa ta zanta da wani malami da ke aiki a jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara, ya koka game da irin rikon sakainar kashin da ake yi wa ilmi.

Wannan malami da bai bari an bayyana sunansa ba, ya ce abokan aikinsu a wasu ma’aikatun sun samu karin albashi tun Juma’a, amma su ba a labarinsu.

Dr. Muhammad Hashim Sulaiman wani ma’aikacin jami’a ne a ABU Zariya, yake fada a Facebook cewa gwamnati ba ta damu da tsaro, ilmi da kiwon lafiya ba.

Dr. Kabiru Danladi Lawanti ya ce a tsawon shekaru takwas, gwamnati mai-ci ba ta taba biyansu albashi kafin 30 ga wata ba, sai a karshen watan Afrilun nan.

Hikimar karin albashi

Tun a baya aka samu labari ma’aikata za su samu inda za su sa kan su bayan an janye tallafin man fetur nan da ‘yan kwanaki, za a kara masu albashi.

Kara karanta wannan

An musu barka da sallah: Sojoji sun yiwa 'yan bindigan Arewa kaca-kaca, sun kashe da yawa

Wani jami’in gwamnati ya ce za a biya har bashin karin na watannin Junairu, Fubrairu da Maris. An tattara karin na 40% ne a albashin Afrilun nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng