Yan Bindiga Sun Sace Kwamishinar NPC Ta Ƙasa a Jihar Ribas
- Kwamishinan hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta jihar Bayelsa ta shiga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Ribas
- Yan bindiga sun tare kana suka yi awon gaba da Misis Gloria Izonfuo, a hanyarta na zuwa Patakwal daga jihar Bayelsa
- Kawo yanzun dai yan sanda sun ce sun bazama neman maharan amma an ce tuni suka nemi miliyan N500m a matsayin fansa
Rivers - Wasu 'yan bindiga da ba'a sani ba sun yi garkuwa da kwamishinar hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) reshen jihar Bayelsa, Misis Gloria Izonfuo.
Daily Trust ta tattaro cewa Izonfuo, tsohuwar shugabar ma'aikatan jihar Bayelsa, ta faɗa hannun yan bindiga ne a mahaɗar titunan Ogbakiri kan Titin gabas maso yamma a jihar Ribas.
Yan bindigan sun yi awon gaba da kwamishinar yayin da take kan hanyar zuwa Patakwal, babban birnin jihar Ribas daga garin Brass na jihar Bayelsa.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace kwamishinar ne tare da Direbanta da kuma yar aikinta a kan hanyar zuwa Patakwal ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu, 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton jaridar punch ya nuna cewa maharan sun sace matar, direba da mai aikinta da misalin ƙarfe 6:30 na yamma ranar Lahadi bayan ta dawo daga ƙarar hukumar Brass.
Shin sun nemi kuɗin fansa?
A halin yanzun wasu bayanai sun nuna cewa masu garkuwa da Misis Izonfuo sun aiko da saƙo, sun nemi miliyan N500m a matsayin kuɗin fansa.
Jami'ar hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ya tabbatar da sace kwamishinar NPC ta ƙasa.
Ya ƙara da cewa kwamishinan hukumar 'yan sandan jihar ya tashi tawaga ta musamman kuma ya ɗora musu alhakin tabbatar da cewa wacce aka sace ta kubuta lami lafiya.
Mahara Suka Kashe Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali
A wani labarin kuma Harin kwantan ɓauna ya yi ajalin manyan jami'an gwamnatin tarayya a ƙasar Mali
Rahotanni daga ƙasar Mali sun bayyana cewa harin ya yi ajalin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa a babban birnin ƙasar da ke yammacin Afirka.
Sai dai har kawo yanzun babu ƙungiyar da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin. Mali na fama da ayyukan ta'addanci wanda ya ta'azzara.
Asali: Legit.ng