Tashin Hankali: Mahara Suka Kashe Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali

Tashin Hankali: Mahara Suka Kashe Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali

  • An halaka shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa a ƙasar Mali, yammacin Nahiyar Afirka a wani harin kwantan ɓauna
  • Bayanai daga babban birnin ƙasar sun nuna cewa harin ya yi ajalin manyan ƙuolsohin gwamnatin riko har su 5
  • Har kawo yanzun ba bu wanda ya fito ya ɗauki alhakin kai wannan hari a Mali, kasar da ke fama da matsalar ta'addanci

Mali - Rahotanni daga ƙasar Mali da ke yammacin nahiyar Afirka sun nuna cewa wasu mahara sun yi ajalin ƙusoshin jami'an gwamnati a wani harin kwantan ɓauna.

Jaridar Aminiya ta rahoto cewa manyan ƙusoshin gwamnatin da aka kashe suna cikin gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin shugaban riko, Kanal Assimi Goita.

Kasar Mali.
Tashin Hankali: Mahara Suka Kashe Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa a Mali Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Bayanai sun tabbatar da cewa yayin wannan sabon mummunan harin, maharan sun kashe Oumar Traore, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da wasu jiga-jigan gwamnati huɗu.

Kara karanta wannan

Bayan Kwashe Shekaru Ana Aiki, Daga Karshe Ministan Buhari Ya Bayyana Ranar Kammala Titin Kaduna-Kano

Bayan haka, direban tawagar jami'an gwmanatin ya ɓata ba bu wanda ya san inda ya ke kawo yanzun sakamakon harin da ya afku a Bamako, babban birnin Mali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Aljazeera ya nuna cewa harin ya auku ne a ƙauyen Nara, wanda ke cikin lardin Koulikoro a kudu maso yammacin Mali, ƙasar da ke cikin nahiyar Afirka ta yamma.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa har kawo yanzun babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin kuma ba'a san waɗanda suka kaddamar da harin, wanda ya lakume rayukan manyan mutane ba.

Ana ganin ƙasar Mali ce a sahun gaba daga cikin jerin ƙasashen yammacin Afrika da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda, wanda ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa.

Najeriya ma na fama da matsalar ta'addanci, kama daga ƙungiyoyin yan ta'adda irinsu IPOB a kudu maso gabas, Boko Haram da ISWAP a arewa maso gabas da 'yan bindiga a arewa ta yamma.

Kara karanta wannan

A Gab da Sallah, Yan Bindiga Sun Halaka Magajin Gari, Sun Aikata Mummunar Ta'asa a Jihar Arewa

Buhari ya yi raddi ga gwamnan Benuwai

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Caccaki Gwamna Ortom, Ya Faɗi Abinda Ya Janyo Masa Rashin Nasara a Babban zaɓen 2023

Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce babu ta yadda mazaunan jihar Benuwai zasu sake aminta da Samuel Ortom saboda ba abinda ya musu tsawon shekara 8.

Buhari, wanda ba ya ga maciji da gwamna Ortom, ya ce gwamnan ke hana FG zuwa kai ɗauki don magance matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262