Hukuncin Addinin Musulunci Idan Bikin Idi Ya Hadu da Sallar Juma'a a Rana Daya

Hukuncin Addinin Musulunci Idan Bikin Idi Ya Hadu da Sallar Juma'a a Rana Daya

  • Akwai yiwuwar Sallar karamar idi ta hadu da Ranar Juma’a a shekarar nan ta 1444 (hijira)
  • Malaman addinin Musulunci sun dade da yin fatawar hukuncin bukukuwan a rana guda
  • Manyan malamai sun rabu gidaje dabam-dabam, an yi sabani a kan hukuncin sallar Juma’a

Kaduna - A nan, mun dauko rubutun da Dr. Kabir Abubakar (Asgar) ya yi a game da wannan mas’ala, za a samu rubutun a shafukansa na Facebook.

Kabir Asgar wanda malamin addini ne a garin Zariya, a jihar Kaduna, ya tsakuro fatawar da Shehin malamin musulunci, Ibn Taimiyyah ya yi a lokacinsa.

An tambayi Sheikhul Islam Ibnu Taimiyah (RahimahulLah) game da wasu mutane guda biyu da suka yi jayayya akan haɗuwar Idi da Juma'a.

Ɗayansu ya ce: wajibi ne ga mutum ya sallaci idin amma ba sai ya je juma'a ba. Ɗayan kuma ya ce zai sallaci duka salloli biyun (Idi da Juma’a)

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Rasa Rayuka Yayin da Wani Gini Ya Tumurmushe Mutane a Abuja Cikin Azumi

Amsar Ibnu Taimiyah:

Godiya ta tabbata ga Allah. Idan sallar idi ta faɗo ranar juma'a malamai suna da maganganu kala uku akai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sallar idi
Sallar idi a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yadda malamai su ka rabu:

1. Mazhabi Na Farko

Wajibi ne a sallaci Juma'a kamar yadda yake wajibi a sallaci idi saboda gama-garin dalilan da suka wajabta salloli biyun.

2. Mazhabi Na Biyu

Juma'a ta faɗi akan mutanen karkara da waɗanda ke zaune a rugage ko anguwannin dake nesa da masallacin Juma'a, saboda halifa Usman Bn Affan (RA) ya yi musu rangwamen cewa za su iya barin juma'a matuƙar sun sami sallar idi.

3. Mazhabi Na Uku

Wanda shine ya fi inganci. Cewa wanda ya yi sallar idi to Juma'a ta faɗi akansa ta fuskar wajibci. Sai dai shi limamin juma'a wajibi ne gare shi ya tsaida sallar Juma'a saboda masu son zuwa juma'a ɗin su sami dama, musamman waɗanda ba su sami idi ba.

Kara karanta wannan

Ba da Mace Nayi Takara ba – Fintiri ya Fadi Asalin Abokan Gwabzawarsa Bayan Ya Zarce

Wannan shine abin da aka samo daga Manzon Allah (SAW) da manyan sahabbansa irin su Umar da Usman da Ibnu Mas'ud da Ibnu Abbas da Ibnuz Zubair da wasunsu (Allah ya yarda da su baki ɗaya). Ba a sami wani ra'ayi da ya saɓa wa wannan daga sahabbai ba.

Malamin ya ce waɗanda suka faɗi zantukan farko da na biyu ba su da masaniya ne game da abin da aka samo daga wajen sahabbai da kuma sunnah.

Idi guda biyu sun haɗu a rana ɗaya a zamanin Manzon Allah (SAW) sai ya sallaci idi sannan ya yi sassauci akan zuwa Juma'a sannan ya ce: "Ya ku jama'a! Kun sami alheri a wannan rana, wanda yake son ya halarci juma'a yana iya halartar ta. Amma dai mu za mu yi Juma'a".

A karshe ya kare da cewa Allah shine mafi sani

Kashe-kashe a Zamfara

Rahoton da mu ka fitar a baya ya nuna ana zubar da jinin Bayin Allah a Zamfara lokacin da al’ummar Musulmai suke dauke da azumi a bakinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Tona Asirin Gidansa, Ya Fallasa Yadda Iyalansa Suka Zaɓi Peter Obi a 2023

‘Yan ta’adda sun aukawa wasu kauyuka a lokacin Sallah, sun ce ba za su daina kai hari ba sai an cire sojojin da aka tura domin kare Birnin Magaji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng