El-Rufai Ya Yabama Dakarun Sojoji Kan Kashe Kasurgumin Dan Bindiga, Isiya Danwasa
- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan kasurgumin shugaban yan bindigar nan da ya addabi al'ummar Kaduna
- Sojoji sun kashe babban dan ta'adda mai suna Isiya Danwasa wanda ya shahara wajen kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma fashin shanu
- Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi jinjina ta musamman ga dakarun rundunar sojin kan wannan namijin kokari da suka yi
Kaduna - Gwamna Nasir Ahmed El-rufai ya yabama dakarun rundunar Operation Forest Sanity (OPFS) kan kashe kasurgumin shugaban yan bindiga, Isiya Danwasa, da suka yi.
Danwasa shine ke da alhakin kashe-kashe da dama, garkuwa da mutane da fashin shanu da ake yi a fadin jihar, Zagazola Makama ya rahoto.
Kasurgumin dan fashin ya hadu da ajalinsa ne yayin wani aikin kautan bauna a Sabon Birni da ke karamar hukumar Igabi.
El-Rufai ya yaba ma dakarun sojojin Najeriya
Gwamna El-rufai ya jinjinawa dakarun bisa aiki da suka yi kan bayanan sirri da kuma aiwatar da hukunci wanda ya kai ga mutuwar Danwasa da hadiminsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnan ya kuma roki jama'a da su ci gaba da bayar da bayanai masu amfani na da kai ga jami'an tsaro, rahoton PRNigeria.
Yan bindiga sun sace matar basaraken Kano da dansa
A wani labari na daban, rundunar yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da sace matar hakimin kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano da dansa.
Rahotanni sun kawo cewa maharan sun farmaki ghidan basaraken inda suka tisa keyar matarsa Halima Kabiru mai shekaru 38 da kuma dansa mai suna Dahiru Kabiru dan shekaru 20.
Da yake nuna takaicinsa a kan al'amarin, kwamishinan yan sandan jihar Kano, Mamman Dauda ya ce sun tura wata tawaga ta musamman don ceto mutanen cikin koshin lafiya.
A wani labarin kuma, mun ji cewa tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da magajin garin kauyen Chida, John Kwayidami da wasu mutane 13 a karamar hukumar Kwali da ke babban birnin tarayya Abuja.
Har wayau, an rahoto cewa maharan sun harbi wani matashi dan shekaru 18 yayin da yake kokarin tserewa daga wajen faruwa al'amarin.
Asali: Legit.ng