Samun 25% Na Kuri'un FCT: Kotu Ta Bada Hukunci Kan Karar Da Mazauna Abuja Suka Shigar Kan Tinubu
- Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da karar da aka shigar na neman dakatar da rantsar da Shugaba Bola Tinubu
- Wasu mazauna Abuja su biyar ne suka shigar da karar da Mai Shari'a Inyang Ekwo ya shi ya yi watsi da ita
- Mai Shari'a Ekwo ya kuma umurci mazauna Abujan su biyar, kowannensu ya biya tarar naira miliyan 10 ga Attoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'a
FCT Abuja - A wani rahoto da ya fito, Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babban Kotun Tarayy da ke Abuja ya yi watsi da karar da aka shigar na neman hana rantsar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin Shugaban Najeriya na 16.
Kamar yadda AIT ta rahoto, wasu mazauna Abuja byar ne suka shigar da karar kan rashin samun kashi 25 cikin 100 na kuri'un Abuja da Tinubu bai yi ba yayin zabe.
Mai Shari'a Ekwo ya ce wadanda suka shigar da karar ba su da hurumin yin hakan kuma a kotun sauraron karar zaben shugaban kasa kawai za a iya shigar da karar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta umurci yan Abuja da suka yi karar Tinubu su biya tarar miliyan 50
Alkalin ya kuma umurci lauyan da ke wakiltan mazauna Abujan biyar, Chuks Nwachukwu ya biya naira miliyan 10 kan kowannensu ga Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari'ar Najeriya.
Mazauna Abujan, Anyaegbunam Okoye, David Adzer, Jeffrey Ucheh Osang Paul, da Chibuike Nwanchukwu, sun shigar da karar ne suna tambaya idan za a iya rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasa duba da cewa bai samu kashi 25 na kuri'un Abuja ba.
Sun kuma nemi a ajiye takardan shaidan cin zabe na Tinubu kuma a hana CJN ko wani jami'in shari'a rantsar da shi shugaban kasa a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Mai shigar da karar ya yi tambaya:
"Shin ko wanda za a zaba shugaban kasar tarayyar Najeriya ya kuma zama shugaban Abuja ta hanun Ministan Birnin Tarayya, a zaben farko yana bukatar samun akalla kashi 25 cikin 100 na kuri'un da aka kada a FCT kamar yadda sashi na 134(2)(b) ya tanada."
Tinubu Ya Ba Lawan Da Gbajabiamila Sabon Aiki Mai Muhimmanci
A wani rahoton kun ji cewa Shugaba Tinubu ya umuri Ahmad Lawan, Shugaban Majalisa ta 9 da Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisa ta 9 su sulhunta rikicin shugabancin majalisa da ke tsakanin yan APC.
Zababben yan majalisar da tsaffi wadanda suka zarce suna ta kai ruwa rana kan batun shiyyar kasar da za ta fitar da sabbin shugabannin majalisa ta 10.
Asali: Legit.ng