An Nemi Tsohon Mataimakin Gwamna An Rasa, Ya Fada Hannun ‘Yan Garkuwa da Mutane

An Nemi Tsohon Mataimakin Gwamna An Rasa, Ya Fada Hannun ‘Yan Garkuwa da Mutane

  • A daren yau aka tabbatar da cewa Onje Gye-Wado ya hadu da sharrin miyaggun ‘yan bindiga
  • Ana zargin wadanda ke garkuwa da mutane sun dauke tsohon mataimakin Gwamnan Nasarawa
  • ‘Yan sanda sun ce an je gidan Farfesa Gye-Wado da ke karamar hukumar Wamba, suka dauke shi

Nasarawa - Onje Gye-Wado wanda ya taba zama Mataimakin Gwamna a jihar Nasarawa, ya samu kan shi a hannun ‘yan bindiga masu yin garkuwa.

Rahoton da Punch ta fitar a safiyar nan ya tabbatar da miyagun ‘yan bindiga sun dauke Farfesa Onje Gye-Wado a yankinsa na Gwagi da ke garin Wamba.

Wani daga cikin ‘yanuwan Onje Gye-Wado ya shaidawa manema labarai cewa a daren Juma’a ‘yan bindigan su ka hauro katanga, suka shigo masa gida.

Miyagun sun fasa tagar dakin mai dakin Farfesa Onje Gye-Wado ne, har su ka samu damar kai gare shi, daga nan su ka tsere da shi zuwa inda ba a sani ba.

Kara karanta wannan

NSCDC Sun Damke Wasu Masu Buga Nairori da Dalolin Karya a Jihar Zamfara

Bayanin 'Danuwan Gye-Wado

Mai dakinsa ta zo gida domin bikin Easter, sai su ka shigo cikin gidan ta tagar dakinta, su ka dauke shi zuwa wani boyayyen wuri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mu na masa fatan jami’an tsaro za su yi kokarin ceto shi ba tare da wani abu ya same shi ba.

- Wata majiya

Jami'an tsaro
Jami'an tsaro a wani kauye Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar nan ta Vanguard ta tabbatar da Onje Gye-Wado wanda ya yi mulki tsakanin 1999 da 2003 ya taba sha da kyar a hannun masu neman dauke shi.

Gye-Wado ya yi mataimakin Gwamna ne a lokacin da Abdullahi Adamu yake mulki a Nasarawa.

Ta tabbata, an yi haka

Kakakin rundunar ‘yan sanda na reshen Jihar Nasarawa, Ramhan Nansel ya tabbatar da labarin garkuwa da dattijon, ya ce su na kokarin kubutar da shi.

DSP Nansel yake cewa mummunnan labarin ya zo masu da kusan karfe 12:30 na dare cewa ‘yan bindiga sun shiga gidan Gye-wado da yake Kauyen Gwagi.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: A Watan Azumi, 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wani Sarki Mai Martaba a Arewa

Da jin labarin, jami’an ‘yan sanda da ke karamar hukumar Wamba su ka shiga bakin aiki, amma kafin su yi wani yunkuri, ‘yan bindigan sun yi gaba da shi.

Masu buga kudin karya

An ji labari NSCDC tayi nasarar cafke wasu masu buga kudin bogi a Zamfara, wadanda aka kama su ne: Kamalu Sani, Uzaifa Muazu da Suleiman Yusuf.

Yadda asirinsu ya tonu kuwa shi ne a ranar 3 ga watan Afrilu 2023 wani ya dauki hayar Keke Napep, sai ya biya shi da kudin jabu, daga nan aka fara bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng