Hamza Yousaf Ya Tabbata Sabon Firayinminista Musulmi Na Farko Na Scotland
- Kasar Scotland ta amarce da sabon Firayinminista Musulmi da aka zaba bayan kada kuri’a a majalisun kasar
- An zabe shi ne bayan samun goyon bayan manyan majalisa da kuma jam’iyyarsa a kasar da ke nahiyar Turai
- A baya, an zabi Rishi Sunak a matsain wanda ya zama sabon Firayinminista a Burtaniya bayan samun goyon baya
Kasar Scotland - An tabbatar da Hamza Yousuf a matsayin sabon Firayinministan Scotland bayan kada kuri’u a majalisar kasar, BBC ta ruwaito.
Hamza ya samu wannan mukamin ne bayan da majalisa da jam'iyyarsa a kasar daga bangarori daban-daban suka bashi mafi yawan kuri’u da ake bukata.
Hamza na da abokan hamayya uku, amma dai sun tsaya takarar ne tare da sanin ba za su iya yin nasara a kansa ba.
Musulmi na farko da ya karbi mukamin kenan
Ya karbi mukamin ne daga hannun Nicola Sturgeon, inda ya zama Firayinminista na shida a kasar kuma dan wata kabila mafi karanci da ke zaune a kasar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Har ila yau, shine wanda ya taba rike mukamin mafi karancin shekaru kuma mai bin tafarkin addinin Islama da zai jagoranci babbar jam’iyyar Burtaniya.
A ‘yan shekarun nan, an fara ganin sauyi a duniyar Turai, inda baki ‘yan kasashen waje ke ci gaba da karbar manyan kujerun tafiyar da harkokin yankin, rahoton France24.
Sunak na Burtaniya ya taya shi murna
Jim kadan bayan da ya lashe zaben, Firayinminista Rishi Sunak ya kira shi a waya tare da taya shi murnar lashe wannan babbar kujerar.
Sunak ya kuma bayyana cewa, a shirye yake ya ci gaba da aiki da gwamnatin Scotland ta fannoni da yawa da suka shafi tattalin arziki da dai sauransu.
Sunak dai shima dan asalin tsatson kasar India ne, amma ya samu damar zama Firayinministan Burtaniya a shekarar da ta gabata, lamarin da ya jawo cece-kuce.
Rishi Sunak ya zama Firayinminista a Burtaniya
A wani labarin, kun ji yadda muka kawo muku rahoton samun damar da Rishi Sunak ya yi na zama Firayinministan Burtaniya a shekarar da ta gabata.
Rishi ya samu wannan mukamin ne bayan samun goyon bayan ‘yan majalisa 100 a wata kwarya-kwaryar zabe da aka gudanar.
Shekarar 2022 da 2023 sun zo da wani sauyi a Turai, inda tsatson baki suka samu manyan mukamai masu ban al’ajabi.
Asali: Legit.ng