Yan Sanda Sun Ceto Mutum 13 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Kogi

Yan Sanda Sun Ceto Mutum 13 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Kogi

  • Yan sanda sun kubutar da wasu bayin Allah 13 da wasu yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kogi
  • Jami'an rundunar yan sanda a Kogi sun yi musayar wuta da wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne
  • Maharan sun tsere bayan sun ji wuta inda yan sanda suka bukaci mazauna yankin Eleite da su kai rahoton duk wani da suka gani da raunin harbi

Kogi - Rundunar yan sandan jihar Kogi ta ce jami'anta sun yi nasarar ceto mutum 13 da aka yi garkuwa da su daga wani Otel da ke yankin Eleite a hanyar titin Lokoja-Ajaokuta.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP William Aya, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, 28 ga watan Maris a Lokoja, ya ce wadanda aka ceton sun hada da maza 11 da mata biyu, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Jami'an yan sanda rike da bindigogi
Yan Sanda Sun Ceto Mutum 13 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Jihar Kogi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da samun rahoton sace mutane sai yan sanda suka bazama aiki

Ya ce lokacin da rundunar ta samu labarin faruwa lamarin, ta tura jami'anta zuwa yankin sannan suka tabbatar da sakin mutanen a ranar Talata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar ta ce:

"Jami'an sashin agajin gaggawa karkashin jagorancin shugabansu, SP Obafemi Ojo, sun shiga aiki nan take bayan samun bayanan sirri sannan suka gano mabuyar masu garkuwa da mutanen a wani daji da ke mararrabar Zariagi-Kabba.
"Da ganin yan sandan, bata garin sun yi musayar wuta da su. Sakamakon wutan da yan sandan suka bude masu, bata garin sun tsere da raunuka daban-daban yayin da aka ceto mutum 13 da aka sace cikin koshin lafiya."

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa an kwato wani kunamar bindigar AK47 da ke dauke da harsasai shida daga wajen da abun ya faru."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Ya bukaci jama'a musamman garuruwan da abun ya shafa da su duba sannan su kai rahoton duk wani da suka gani dauke da harbin bindiga ofishin tsaro mafi kusa, rahoton Punch.

Yan sanda sun hana yin zanga-zanga a jihar Nasarawa

A wani labari na daban, rundunar yan sanda a jihar Nasarawa ta sanar da wani sabon doka na hana gudanar da zanga-zanga a fadin jihar a kokarinta na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng