Hukumomin Saudiyya Sun Gargadi Masu Dauke-Dauken Hotuna a Lokacin Ziyarar Hajji da Umrah

Hukumomin Saudiyya Sun Gargadi Masu Dauke-Dauken Hotuna a Lokacin Ziyarar Hajji da Umrah

  • Ba sabon abu bane ganin Mahajja da masu ziyarar Umrah suna yada hotuna da bidiyo a kafafen sada zumunta
  • Hukumomin Saudiyya sun bayyana kudurin daukar mataki kan irin wadannan mutane, tare da jan hankalinsu a kai
  • Malamai suna kan ra’ayin cewa, ‘Riya’ ne zuwa wurin ibada tare da daukar hotuna ana yadawa a kafar sada zumunta

Kasar Saudiyya - Yayin da ake tururuwa zuwa aikin Umrah, hukumomin Saudiyya sun gargadi masu ziyara a wannan shekarar, rahoton BBC.

Hukumar kula da aikin Hajji da Umrah ta bayyana cewa, akwai bukatar jama’a su ke daraja wuraren ibada masu alfarma a ziyarce-ziyarcensu.

Wannan na zuwa ne tare da bayyana bukatar a bi dokokin da hukumar ta gindaya wajen takaita daukar hotuna a masallatan Haramin guda biyu.

An gargadi masu daukar hotu a masallacin Harami
Yadda jama'a ke daukar hoto a Harami | Hoto: geo.tv
Asali: UGC

A cewarta, abu ne mai muni a ga tarin Musulmi sun shagala da daukar hotuna a madadin mai da hankali kan yin ibadar da ta kawo su kasa mai tsarki.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A daina daukar hoton wasu jama’a ba tare da izininsu ba

A bangare guda, hukumar ta bayyana gargadi kan jama’a da su guji hadawa da wasu mutanen da babu ruwansu a cikin hotunansu ba tare da izini ba.

Wannan na nufin, an hana jama’a daukar hotuna a wurare masu cunkoson jama’a, inda hukumar tace hakan na kara yawan cunkoso a masallatan, rahoton Saudi Gazette.

Yayin da kafafen sada zumunta suka zama filayen baje-kolin iya yi a duniya, jama’a sun bullo da sabuwar dabi’ar daukar hotuna a ziyarar ibada a kasar ta Saudiyya.

Hakan ‘Riya’ ne, inji Malamai

Ba sabon abu bane ganin mahajjata da masu ziyarar Umrah suna daukar hotuna tare da daurawa a shafukan sada zumunta.

Malamai da yawa na kan ra’ayin cewa, wannan dabi’a ta yada hotunan wurin ibada ba komai bane face ‘Riya’, ma’ana yin ibadar don wasu mutane su gani.

Kara karanta wannan

Toh fa: DSS ta hango matsala a Najeriya, ta ba 'yan kasa shawarin kariya

Sheikh Shuraim ya daina limanci

A wani labarin, Ash-Sheikh Saud Shurain na Masallacin Harami ya daina limanci bayan shafe akalla shekaru 30 yana wannan aikin.

Wannan na zuwa ne bayan da aka bayyana sunayen limaman da za su ja sallar Tarawi na wannan watan Ramadanan, babu sunansa a ciki.

A baya an ruwaito cewa, daya daga cikin limaman masallacin Haramin zai yi ritaya daga jan sallah a masallatan biyu masu tsarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.