Gwamna Ya Rattaba Hannu a Kan Yarjejeniya Domin a Daina Daukewa Jiharsa Lantarki
- Idan aka yi dace, dauke wutar lantarki zai zama wani bakon lamari a manyan biranen Anambra
- Gwamnatin jihar Anambra ta shiga yarjejeniya ta MoU da kamfain EEDC domin wuta ta zauna
- Charles Chukwuma Soludo ya ce tun kafin ya zama Gwamna yake da wannan burin a cikin rai
Anambra - Gwamnatin jihar Anambra ta sa hannu a yarjejeniyar MoU da kamfanin raba wuta na Enugu (EEDC) domin inganta wutar lantarki.
The Cable ta kawo rahoto cewa an shiga wannan yarjejeniya a ranar Juma’a da ta wuce da nufin inganta wutar lantarkin da ake samu a Anambra.
Mai girma Charles Chukwuma Soludo da Julius Emeka suka rattaba hannu a madadin jihar Anambra, sai Emeka Offor a madadin EEDC.
Sakataren yada labaran gwamnan jihar Anambra, Christian Aburime, ya ce makasudin shi ne mutane su rika samun lantarki babu kiftawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Christian Aburime ya fitar da jawabi
A yau na rattaba hannu a kan yarjejeniyar MoU da kamfanin raba lantarki na EDDC domin tabbatar da cewa ana samun wuta awa 24 a rana, sau bakwai a mako.
An yi wannan sa hannu ne a dakin taron zartarwa da ke gidan gwamnati a birnin Awka. Yau rana ce mai tarihi ga daukacin mutane da kuma jihar Anambra.
Wannan yarjejeniya za ta kawo sauyi na kwarai wanda zai taimaka wajen samun dadin rayuwa domin ba za a ji dadin zama ba tare da wutar lantarki ba.
Da dadewa kafin zama Gwamna, na fahimci muhimmancin wuta da yadda za a iya samar da wuta a kankanin lokaci a akalla manyan birane uku zuwa hudu.
Za a noma abin da aka girba
A jawabin Christian Aburime, an ji Farfesa Charles Chukwuma Soludo yana cewa tun bara ya fara wannan kokari, sai a yanzu ne wannan batun ya tabbata.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Mai girma Gwamnan yana neman kwadaito da Attajiran Anambra su dawo da dukiyarsu cikin jihar. This Day ta fitar da rahoton a ranar Lahadi.
Da yake magana, shugaban kamfanin EEDC, Julius Emeka ya ji dadin wannan yarjejeniya, yana farin cikin fitar da mutanen Anambra daga duhu.
EFCC ta shiryawa Gwamnoni
Nan da ranar 29 ga watan Mayun 2023, wasu gwamnoni za su bar ofis, an ji labari Abdulrasheed Bawa ya ce hukumarsa ta EFCC ta dana masu tarko.
Abdulrasheed Bawa ya nuna ban da Gwamnoni, akwai wasu Ministocin kasar da ake bincike kan su, da zarar an kammala komai, daga nan sai a tafi kotu.
Asali: Legit.ng