Albarkacin Ramadan: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Wa Ma'aikata Awannin Aiki

Albarkacin Ramadan: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Wa Ma'aikata Awannin Aiki

  • Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage wa ma'ikatan gwamnati awannin aiki saboda albarkacin watan Ramadan
  • A wata sanarwa da shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar ta hannun mai magana da yawunsa ya fitar, gwamnatin ta ce anyi hakan ne don ba wa ma'aikata damar shirin bude baki
  • Sanarwar ta kuma bukaci ma'ikatan da su sanya jihar a addu'o'in zaman lafiya da karin yalwar tattalin arziki

Jihar Jigawa - Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage awannin aikin gwamnati a jihar da awa biyu lokacin azumin watan Ramadan na shekarar 2023, rahoton The Punch.

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan jihar, Hussaini Kila ya raba wa manema labarai ta hannun mai magana da yawunsa, Ismail Dutse.

Taswirar Jigawa
Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma'aikata awannin aiki saboda azumin Ramadan. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

A cewar sanarwar, ma'aikatan gwamnati za su zo aiki da misalin 9:00 na safe su kuma tashi 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis maimakon 5:00 na yamma.

Kara karanta wannan

A shirye nake: Zababben gwamnan Katsina ya fadi abin da zai a ranar da ya karbi mulki

''Sanarwar ta cigaba da cewa, ma'aikata za su zo aiki a ranar Juma'a da misalin 9:00 na safe su kuma tashi 1:00 na rana kamar yadda aka saba,'' in ji shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin rage wa ma'aikatan Jigawa lokacin aiki

Ya yi bayanin cewa an yi hakan ne don bawa ma'aikatan jihar damar shirin buda baki da kuma samun karin lokacin ibada a wannan wata mai girma.

Gwamnatin ta ce ta na fatan ma'aikatan za su yi amfani da lokacin Ramadan don neman shiriya da kuma nema wa jihar albarka.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana:

''Ana kuma fatan ma'aikatan gwamnati za su yi amfani da lokacin azumi don yi wa jihar addu'ar zaman lafiya da karuwar tattalin arziki da ma yi wa kasa addu'a ba ki daya''.

Jami'an Hukumar Hisbah a Kano sun shiga daki-daki don neman masu yin ayyukan badala a jihar

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-ɗumi: Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Hadimin Gwamnan Arewa, Bayanai Sun Fito

A wani rahoton daban, kun ji cewa jami'an hukumar ta Hisbah a Jihar Kano sun yi wan bincike na mai zaman kansa inda suka rika shiga dakuna daban-daban a Hills anda Valley, wani wajen shakatawa da bude ido a Dawakin Kudu da ke Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel