Magidanci Ya Rabu Da Matarsa Bayan Ya Gano Tana Da Wasu Masoya 2 Bayan Shi

Magidanci Ya Rabu Da Matarsa Bayan Ya Gano Tana Da Wasu Masoya 2 Bayan Shi

  • Wata matashiyar mata ta bayyana yadda aurenta ya mutu bayan mijinta ya gano tana cin amanarsa da wasu maza biyu
  • A cewarta, tsohon mijinta ya san tana cin amanarsa amma bai san cewa da maza biyu bane
  • Abun bakin ciki, da ya gano, sai mutumin ya fusata da ita kuma ya zama bai da zabi da ya wuce rabuwar aurensu

Wata matashiyar mata a Twitter mai suna MrsKhandiCoated ta bayyana yadda ta rasa mijinta da saurayinta a rana guda.

A cewarta, mijinta, wanda ya yanzu sun rabu, ya san cewa tana cin amanarsa da wani, amma ya yi kokarin shanye zunubin da take aikatawa.

Wata mata duke cikin damuwa
Magidanci Ya Rabu Da Matarsa Bayan Ya Gano Tana Da Wasu Masoya 2 Bayan Shi Hoto: Jamie Grill
Asali: Getty Images

Sai dai kuma, a wata rana, tsohon mijinta ya kira saurayinta sannan ya fada masa cewa ya dawo da ita gida.

Sai saurayinta ya mayarwa tsohon mijinta martani, yana mai bayyana cewa bata tare da shi domin shima ta yi masa karyar cewa za ta kasance tare da mijinta a wannan ranar.

Kara karanta wannan

Ina gamsar dasu: Bidiyon matar da ta auri maza 3, take rayuwa dasu a cikin gida daya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutanen biyu sun hada baki sannan suka dungi gasa ta har sai da ta yarda cewa tana tare da saurayinta tun tana budurwa. Wallafar da ta yi a Twitter ya haddasa cece-kuce sosai a soshiyal midiya.

Ta rubuta:

"Dambarwar karshe a aurena na farko shine lokacin da tsohon mijina ya kira saurayina sannan ya fada masa cewa abun ya zo karshe yau ya dawo da ni gida yanzu sannan saurayina ya fada masa cewa ina tare da shi yau...sai su biyun suka dungi gasa ni har sai da na yarda cewa ina tare da tsohon saurayina na tun ina budurwa.. an ga hauka a wannan ranar."

Ga wallafar a kasa:

Jama'a sun yi martani

@indy_ugh ya rubuta:

"Yallabai matarka tana cin amanarmu."

@SkylerB97 ya rubuta:

"Na karanta abubuwa masu daga hankali sosai a nan amma babu wanda ya doke wannan."

Kara karanta wannan

Magidancin Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske, Ya Ce An Gina Auren Ne Kan Soyayyar Juna

@Nyx_19 ya yi martani:

"Sannu da aiki."

@naturalhairrule ta ce:

"Idan ba za ki iya fadawa saurayinki gaskiya ba wa za ki fadawa gaskiya?"

@Tae23 ya ce:

"Ba zan yarda da wata mace ba daidai da rana daya a rayuwata saboda wannan wallafar."

Magidanci ya nemi yan bakin ciki su kyale shi ya ci amarci da matarsa

A wani labari na daban, wani magidanci da aka zarga da auren yarinyar yar shila ya ce babu wanda ya yi wa matarsa auren dole ita ta zabe shi kuma yana sonta. Ya kuma bayyana cewa shekarunta 21.

Asali: Legit.ng

Online view pixel