Wata Malamar Makaranta Ta Fada Soyayya da Dalibi, Ta Saki Bidiyo

Wata Malamar Makaranta Ta Fada Soyayya da Dalibi, Ta Saki Bidiyo

  • Wata Malamar makaranta ta girgiza soshiyal midiya yayin ta bayyana yadda alakar soyayya ta kullu tsakaninta da tsohon ɗalibinta
  • A wani bidiyon hotunan da ta wallafa, ta baiwa mutane mamaki bayan tace ta koyar da shi a makarantar Firamare a wasu shekaru da suka shige
  • A cewarta, ta raine shi har ya girma kuma tana samun farin ciki a soyayyarsu, kuma a cewarta ba ta dana sani

Wata malama da take soyayya da tsohon ɗalibinta na makarantar Firamare ta haddasa kace-nace a soshiyal midiya.

Soyayyar zankadediyar malamar da ɗalibinta ta fito fili ne bayan ta wallafa bidiyon Hotunan soyayyarsu a dandanlin sada zumunta watau TikTok.

Soyayyar malama da Dalibi.
Wata Malamar Makaranta Ta Fada Soyayya da Dalibi, Ta Saki Bidiyo Hoto: @_blackbird_01
Asali: TikTok

Malamar ta bayyana yadda take shan soyayya da ɗalibinta kuma ta labarta asalin yadda ƙauna ta shiga tsakaninsu tun asali.

Matar mai shafin @_bƙackbird_01 ta wallafa Hotunan da suka yi a baya, tana cewa, "Daga malamar makarantar Firamare zuwa masoya."

Kara karanta wannan

“Karku Rantsar da Tinubu Domin Yin Hakan Ya Sabawa Dokar Tsarin Mulkin Najeriya” - Baba Ahmed

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamanta ta ce:

"Na raine shi tun yana ƙarami har ya girma."

Da yawan mutane sun nuna tantama kan labarin soyayyar malamar, wasu kuma suka mata shagube amma matar ta tsaya kan bakarta.

Malamar ta maida martani ga ɗaya daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta, inda ta faɗa masa cewa:

"Mutane da yawa zasu tsane ni kamar na yi wani sabon abu. Ina cikin farin ciki kuma ban yi nadamar abinda na aikata ba."

Kalli bidiyon a nan ƙasa

Martanin mutane a soshiyal midiya

Mask Man ya ce:

"Wai kina nufin soyayya kike da ɗalibinki na makarantar Firamare?"

Karatus ya rubuta cewa:

"Wannan ai sa'an ƙaninki ne meyasa baku ɗauki Hoto a cikin aji ba."

Sammy Prize ta ce:

"Wannan labarin bai da kai ko dai ni kaɗaine ban fahimta ba."

Kara karanta wannan

Batun Hango Ranar Mutuwar Sa, Shahararren Fasto Ya Fito Ya Bayyana Gaskiyar Zance

Oyinlola ya ce:

"Maganar gaskiya ban fahimci abinda ke wakana ba a nan."

A wani labarin kuma Dan Najeriya Da Aka Zarga Da Auren Karamar Yarinya Ya Yi Karin Haske Kan Shekarun Amaryarsa

Mutumin mai suna Aminu Ɗanmaliki ya ce zargin da ake ya auri ƙaramar yarinya ba gaskiya bane domin amaryarsa ta kai shekaru 21 a duniya.

A cewarsa, shi da ita suna kaunar junansu ba auren dole aka mata ba. Mutane da yawa sun maida masa martani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel