Daga Sanarwar Ya Lashe Zabe, Gwamna Ya Bada Umarnin Karawa Ma’aikata Albashi

Daga Sanarwar Ya Lashe Zabe, Gwamna Ya Bada Umarnin Karawa Ma’aikata Albashi

  • Sanarwa ta fito cewa Babajide Sanwo-Olu ya yi na’am da a fara yi wa ma’aikata karin albashi
  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bada umarnin karin 20% da aka yi ya fara aiki daga Junairu
  • Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Legas ya tabbatar da wannan a wata sanarwa da ya fitar

Lagos - A ranar Litinin, 20 ga watan Maris 2023, Babajide Sanwo-Olu ya bada umarnin a fara dabbaka karin albashin da ya yi wa ma’aikatan Legas.

A rahoton Vanguard ne aka fahimci Mai girma Mista Babajide Sanwo-Olu ya amince da cewa karin 20% da aka yi wa ma’aikatan jihar Legas zai soma aiki.

Wadanda karin kudin ya shafa sun hada da masu aikin gwamnati, ma’aikatan kananan hukumomi da duk ma’aikatan da ke karkashin hukumar SUBEB.

Sabon tsarin albashin zai soma aiki tun daga watan Junairun 2023. A karshen watan nan na Maris za a biya ma’aikatan jihar bashin cikon albashin Junairu.

Kara karanta wannan

Azumin bana: Sarkin Musulmi ya fadi ranar da ya kamata a fara duban jinjirin wata

Punch ta ce bashin albashin watan Fubrairu zai shigo cikin albashin Afrilu da za a biya nan gaba.

Sanwo Olu
Babajide Sanwo Olu wajen kamfen APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakeem Muri-Okunola ya fitar da takarda

Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Legas, Mr Hakeem Muri-Okunola ya sanar da hakan a sanarwar da aka fitar a ranar Litinin 20 ga watan Maris 2022.

Takardar da ta fito daga ofishin Hakeem Muri-Okunola ta ce duk wasu Akantoci su ba sanarwar muhimmanci, kuma su yada ta sosai zuwa ga inda ta dace.

“Ana masu sanar da cewa a yunkurin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na inganta walwalar ma’aikatan gwamnatin Legas, ya amince da karin albashi ga ma’aikatan da ke aikin gwamnati, aikin kananan hukumomi da hukumar SUBEB ta jiha.
An yi kari da kashi 20% wanda zai soma yin aiki daga Junairun 2023.

- Hakeem Muri-Okunola

Muri-Okunola yake cewa wannan mataki da aka dauka ya nuna gwamnati mai-ci ta damu da halin ma’aikata, aka nemi su dage wajen yi wa jiha aiki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Harin Wurin Raba Kayayyakin Zabe, Sun Tafka Barna

Sanata Chimaroke Nnamani

Bayan tsawon lokaci a PDP, rahoto ya zo a farkon makon nan cewa Chimaroke Nnamani ya zabi ya fice daga babbar jam’iyyar hamayyar Najeriya

Tsohon Gwamnan ya tabbatar da hadewarsa da zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, dama shi ya marawa baya a maimakon Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng