An Sake Bindige Wani Jigon Jam'iyyar PDP Har Lahira A Rumfar Zabe

An Sake Bindige Wani Jigon Jam'iyyar PDP Har Lahira A Rumfar Zabe

  • Oyibo Nwani, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party kuma wakilin jam'iyyarsa a zaben gwamna da yan majalisar jiha ya zama mutum na biyu da yan bindige suka harbe har lahira yayin zabe
  • Lamarin ya faru ne a rumfar zabe yayin da wasu mahara da ake zargin sun taho sace akwatin zabe da wasu kayayyaki suka kawo hari, suka fara dambe da matasa da masu zabe
  • SP Onome Onovwakpopyeya, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi ya tabbatar da afkuwar hayaniyar da ta faru a rumfar zaben tare da mutuwar jigon na PDP

Jihar Ebonyi - Wasu da ake zargi yan daban siyasa ne sun bindige, Oyibo Nwani, jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, kuma wakilin jam'iyya a zaben gwamna da majalisar dokokin jihar Ebonyi har lahira a rumfar zabensa da ke karamar hukumar Onicha.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

The Punch ta rahoto cewa karamar hukumar Onicha ce garin da Chief Ifeanyi Odi, dan takarar gwamna na PDP ya fito.

Ebonyi
An Sake Bindige Wani Jigon Jam'iyyar PDP Har Lahira A Rumfar Zabe. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa yan daban da ake zargin sun taho sace akwatinan zabe ne da wasu kayan zabe a yayin da matasa da sauran masu zabe suka yi kokarin fatattakar su.

An yayin da ake arangama tsakanin masu zaben da yan daban, maharan sun harbi jigon na jam'iyyar PDP, yayin da ya ke kankame da akwatin zaben a hannunsa.

Martanin yan sanda

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ebonyi, SP Onome Onovwakpopyeya ya tabbatar da afkuwar hatsaniyar tare da kashe jigon na jam'iyyar PDP.

Jam'iyyar PDP ta ce za ta tafi kotu kan sakamakon zaben gwamnan Katsina

A wani rahoton, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta ce ba ta amince da sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar Asabar 18 ga watan Maris ba, tana mai cewa za ta garzaya kotu.

Kara karanta wannan

Buri ya cika: Daga cin zabe, sabon gwamnan Sokotomya fadi abubuwa 9 da zai yi

Dakta Mustapha Inuwa, shugaban kwamitin yakin neman zaben Atiku/Lado ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai da ya kira ranar Litinin 20 ga watan Maris a Katsina, babban birnin jihar.

Inuwa ya kara da cewa an samu tashin hankali yayin zaben, bata suna da tilasawa da wasu nau'ikan magudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164