Yan Sanda Sun Kama Shahararren Dan Majalisar Kano Kan Yunkurin Kona Ofishin INEC

Yan Sanda Sun Kama Shahararren Dan Majalisar Kano Kan Yunkurin Kona Ofishin INEC

  • Rundunar yan sandan Jihar Kano ta yi bajakolin wanda ta kama da laifuka daban daban a lokacin gudanar da zabukan gwamna da na yan majalisar jiha
  • Cikin wanda rundunar ta gabatar, akwai dan majalisar jiha mai wakiltar Gezawa, Isyaku Ali Danja da ake zargi ta jagorantar yan daba don yunkurin kona hukumar zabe
  • Rundunar ta bayyana cewa da zarar ta kammala bincike zata gabatar da mutanen sama da 160 a gaban shari'a don girbar abin da suka shuka

Kano - Rundunar yan sandan Jihar Kano ta tsare Isyaku Ali Danja, tare da wasu, daga mazabar Gezawa bisa zargin jagorantar yan daba don lalata cibiyar tattara sakamakon zabe ta hukumar INEC a karamar hukumar Gezawa da ke Jihar Kano, rahoton Vanguard.

Kwamishinan yan sandan jihar Hussaini Muhammad Gumel ne ya bayyana haka ranar Lahadi lokacin da ake bajakolin kusan mutum 164 bisa zargin aikata laifuka daban daban yayin da a ke gudanar da zaben gwamna da na yan majalisar jiha da aka kammala a baya bayan nan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Saka Dokar Hana FitaDaga Safe Har Dare

Suspects in Kano
Yan Sanda Sun Kama Dan Majalisar Kano Kan Yunkurin Kona Ofishin INEC. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kwamishinan ya bayyana cewa daga ciki akwai wanda ake zargi da satar akwatu, tarwatsa zabe, tada fitini ta hanyar mugayen makamai da kuma ta'amalli da miyagun kwayoyi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bada tabbacin za a gudanar da bincike tare da gabatar da su gaban shari'a don girbar abin da suka shuka.

Ya ce:

''A kokarinmu na tabbatar da zaman lafiya a zaben gwamna da na yan majalisar jiha a fadin jihar nan mu na gabatar da mutanen da mu ke zargi da aikata laifuka daban daban lokacin zaben.
''An kama su saboda satar takardun zabe, tarwatsa zabe, yawo da miyagun makamai, wasu kuma an kama su miyagun kwayoyi.
''Daga cikin wanda mu ka kama akwai dan majalisar jiha Isyaku Ali Danja na Gezawa, wanda ya jagoranci tawagar yan daba da yunkurin kona cibiyar tattara sakamakon zabe ta INEC a Gezawa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jami'in Tattara Sakamakon Zabe A Kano Ya Yanke Jiki Ya Fade A Hedkwatar INEC

''Za mu binciki dukkansu mu kuma mika su kotu''

Kwamishinan ya kuma yi kira ga daukacin al'umma da su bai wa yan sanda hadin kai don tabbatar da ba a yi shagalin murnar cin zaben da ya saba da doka ba.

An samu rashin jituwa tsakanin wakilan jam'iyyar PDP da APC a Ogun

Wakilan jam'iyyar All Progressives Congress, APC da na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, sun yi rikici a ranar Lahadi 19 ga watan Maris a cibiyar tattaro sakamakon zaben gwamnan jihar Ogun na 2023.

Rikicin ya samo asali ne yayin da jam'iyyar APC ta dage cewa wakilai uku za ta tura wurin tattara sakamakon zaben amma wakilin PDP ya ki yarda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164