Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 60 da Ke Kokarin Farmakar Cibiyar Tattara Sakamakon Zabe a Borno
- Rahoton da muke samu ya bayyana yadda ‘yan ta’addan ISWAP suka kai farmaki sansanin soja a wani yankin jihar Borno
- An ce sun yi yunkurin lalata aikin tattara sakamakon zaben gwamna da aka yi a jihar, amma basu yi nasarar hakan ba
- An naqalto yadda sojoji suka hallaka 60 daga cikin ‘yan ta’addan, suka kwato makamai da sauran kayan aikata laifi
Jihar Borno - Sa’o’i kadan bayan gwamna Babagana Zulum na Borno ya kada kuri’arsa a gundumar Ajari da ke karamar hukumar Mafa, sojoji suka hallaka wasu ‘yan ta’addan ISWAP 60 nan take.
Rahoton da muka samo daga kafar labarai ta Channels Tv ya ce, ‘yan ta’addan sun so hargitsa cibiyar tattara sakamakon zabe da ke jihar ne a ranar 18 ga watan Maris na zaben gwamnoni.
Ku rantse za ku zabe mu: Yadda 'yan siyasa ke yarjejeniya da jama'a kafin siyan kuri'unsu da taliya a Neja
Kasancewar akwai sojoji a wurin, ‘yan ta’addan sun gamu da ajalinsu yayin da sojojin suka tsaya tsayin daka don kare cibiyar tattara sakamakon zaben kuma sansaninsu.
Yadda ‘yan ta’addan suka dura garin Mafa
Rahotanni daga gidan soja sun bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun dura garin Mafa ne a motoci dauke da muggan makamai da misalin karfe 2:00 na dare, inda suka tunkari sansanin sojan kai tsaye, inda ake tattara sakamakon zaben.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sojojin da ke aiki a rundunar Operation Hadin Kai sun dakile harin, inda sojin sama suka tarwatsa tawagar ‘yan ta’addan da bama-bamai ta sama.
An ruwaito cewa, an kashe ‘yan ta’addan da yawa, yayin da wasu kuma suke tsere da raunukan harbin bindiga daga ruwan wutan soja.
Wata majiya ta shaida cewa, an tsinci gawarwakin ‘yan ta’adda 60. Hakazalika, an tattaro wata mota Hilux da makamai masu yawa da ‘yan ta’addan suka tsere suka bari.
Yadda irin haka ya faru a zaben shugaban kasa da ya gudana a watan jiya
A wani labarin, kun ji yadda jami’an sojojin Najeriya suka dakile harin ‘yan ta’adda a jihar Borno da ke kokarin kawo tsaiko ga aikin zaben shugaban kasa da aka yi.
Hakazalika, an dakile wasu ‘yan daban da suka so kawo tsaiko ga zaben a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya a watan jiya.
Rahotanni sun bayyana yadda zabukan Najeriya suka kasance da kuma yadda ‘yan daba da ‘yan ta’adda ke kawo tsaiko ga zabukan.
Asali: Legit.ng