PDP Ta Lallasa APC, Lashe Kujerar Majalisar Dokokin Jiha Ta Farko a Jihar Kogi
- Rahoton da muka samu ya bayyana yadda jam'iyyar PDP ta samu kujerar farko a zaben majalisar wakilai a jihar Kogi
- jihar Kogi na daga daga cikin jihohin da jam'iyyar APC ke mulki kuma ke kan gaba wajen yada akidun APC a Najeriya
- Zaben bana ya zo da abubuwan ban mamaki, wadanda ba a tsammani da yawa sun lashe zaben kujeru
Dan takarar jam'iyyar PDP daga karamar hukumar Ogori Magongo a jihar Kogi, Bode Ogumola ya lashe kujerar majalisar dokokkin jiha da aka yi a jiya Asabar.
Baturen zabe na hukumar INEC, Mr. Ekundayo Mejebi ne ya sanar da sakamakon zaben a cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Magnongo da safiyar yau Lahadi 19 ga watan Maris.
Ya bayyana cewa, dan takarar na PDP ya lashe zaben ne da kuri'u 2,910, inda ya banke abokin hamayyarsa na APC, wanda ya samu kuri'u 2,162.
Matasa sun kunyata manyan 'yan siyasan Najeriya
A bangare guda, kunji yadda siyasar bana ta zo da sabon salo, yadda matasa suka mamaye kujeru da yawa a wasu yankunan kasar a zaben bana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rasheed Buruji Kashamu, wani matashin dan takarar majalisar Ijebu ta jihar Ogun ya lashe zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, rahoton Daily Trust.
Wani matashin na daban, Yusuf Amosun ya lashe zaben majalisar wakilai a jihar Ogun, a karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Rukayat Motunrayo Shittu a jihar Kwara ta taka rawar gani yayin da doke abokin hamayyarta dan takarar jam'iyyar PDP.
Wadannan kadan daga cikin matasan da suka taka rawar gani kenan a zaben 2023 na 'yan majalisar wakilai a Najeriya.
Gwamna Buni na Yobe ya sake lashe zabe
A wani labarin, kun ji yadda gwamna Buni ya sake samun damar lashe zaben gwamna, inda ya koma a wa'adi na biyu na mulki a wannan shekarar.
Buni ya gwabza ne da 'yan takarar jam'iyyu da yawa, ciki har da PDP, babbar jam'iyyar adawa a Najeriya.
Ana ci gaba da tattara sakamakon zaben jihohi daban-daban na Najeriya bayan kammala kada kuri'u a zaben na bana ranar 18 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng