Jam’iyyar Labour a Ogun Ta Kulla Kawance da PDP Don Lallasa Gwamna Abiodun a Zaben Gobe
- Dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP ya samu karbuwa yayin da jam’iyyar Labour ta bayyana goyon bayanta gareshi
- Wannan lamarin ya kawo tsaiko a Labour, inda wani tsagin jam’iyyar ya mara wa gwamna mai ci baya
- Saura kasa da sa’o’i 24 a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun dokokin jihohi a Najeriya, har da jihar Ogun
Jihar Ogun - Kasa sa’o’i 24 a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a Najeriya, jam’iyyar Labour a jihar Ogun ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Punch ta ruwaito.
Gamewar jam’iyyun biyu an ruwaito cewa, zai zama hadin gwiwa ne don tabbatar da tsige gwamna mai ci a jihar kuma dan takarar gwamnan APC.
A bangare guda, wani tsagin jam’iyyar ta Labour ta bayyana goyon bayanta ga gwamna Abiodun a zaben mai zuwa gobe.
Ana Dab Da Zabe, Gwamnan APC Mai Neman Tazarce Ya Samu Tagomashi, Dan Takarar Gwamna Ya Janye Masa Takara
Amma, jam’iyyar karkashin shugabanta na riko a matakin kasa ta yi Allah-wadai da yadda tsaginta ya goyi bayan gwamnan na APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar da jam’iyyar Labour ta fitar
A cikin wata sanarwar da shugaban kwamitin rikon na Labour ya fitar a ranar Juma’a ta hannun sakataren yada labaran kwamitin, Tokunbo Peters, ya ce dan takarar gwamnan PDP, Ladi Adebutu Labour ke goyon baya.
Jam’iyyar ta ce, ta zabi dan takarar na PDP ne saboda itace jam’iyyar da suke da alaka mai karfi da ita da manufofi iri daya, Within Nigeria ta tattaro.
A cewarta, jam’iyyu da yawa sun nuna sha’awar hada gwiwa da Labour saboda ganin yadda ta samu karbuwa gabanin zaben gwamna a jihar.
Ta kuma yi karin haske da cewa, ta zabi PDP ne saboda manufofi, hange da akidunsu iri daya ne da jam’iyar ta Labour.
2023: Jam'iyyar Accord Party Ta Balle Daga Hadakarta Da Jam'iyyar Peter Obi, Ta Koma Bayan Gwamnan APC Mai Neman Tazarce
Za a yi zaben gwamnoni, za kuma a hada da na sanatoci a waus jihohi 15
A wani labarin, kunji yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce za a yi zaben sanatoci a wasu mazabun kasar nan a gobe Asabar 18 ga watan Maris.
Wannan ya faru ne sakamakon tsaikon da aka samu a ranar zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka yi a watan Faburairun da ya gabata.
Ya zuwa yanzu, jam’iyyun siyasa da sauran ‘yan siyasa da hukumar zabe na ci gaba da shirin zaben da za a yi a gobe Asabar.
Asali: Legit.ng