An Gano Amaryar da Dattijo Ya Aura Ba Ta Yau Bace, Ashe Ma Bazawara Ce
- Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan auren wata amarya da wani dattijo, gaskiyar zance ya fito, an yi walkiya, an gano komai
- Sakina, wata dalibar jami’a ce ba karamar yarinya kamar yadda wasu suke zato ba, kuma an ce bazaware ce da ta yi aure ta fita
- Ba sabon abu bane ake ganin auren babba da yarinya, ko yaro da babbar mace ba a Najeriya, ya sha faruwa sau da yawa
Jihar Bauchi - An shiga cece-kuce a kafar sada zumunta a Najeriya biyo bayan ganin wani bidiyon da ya shahara na auren wani dattijo da matashiyar amaryasa.
‘Yan gulman kafar sada zumunta sun gaza hakuri, inda da yawa suke cewa amaryar ta yi kankanta da aure, wasu kuwa na cewa, ko da ma babba cewa, mijin nata ai ya zama kaka.
Sai dai, da alamu wannan amarya dai ba yarinya bace, kasancewar ta yiwu tana da kananan shekarun da gaske, amma dai ba ta yau bace.
Wasu na ta yada batun cewa, amaryar bata ma haura shekaru 12 ba, wasu kuma na kan ra’ayin a dai bincika a gano tushen batun.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abin da aka binciko aka gano
A binciken da jaridar Aminiya tace ta yi, ta tattaro cewa, amaryar sunanta Sakina Musa Waziri, kuma ba kamar yarinya ce kamar yadda ake tsammani.
An gano cewa, wannan amarya shekaranta sun kai 21, kuma bazawara ce da shi wannan dattijon ya samu ya yi wuf da ita.
An kuma gano cewa, dattijon da ya angwance ba kowa bane face Dan Malikin Bauchi, Alhaji Aminu Muahmmad.
Wacece amaryar?
A cewar Aminiya, amaryar mai suna Sakina ‘yar asalin jihar Bauchi ce, an haife ta a Unguwar Railway da ta shahara a jihar.
Mahaifinta kuwa, wani tsohon alkali ne da ake kira Malam Musa Waziri, shi ma dan asalin jihar Bauchi ne.
Sakina ta shiga jami’ar jihar Bauchi da ke garin Gadau kafin ta yi amarcewar farko, inda aka ce auren bai dade ba ta rabu da mijin.
Yanzu dai Allah ya hada ta da mai girma Dan Maliki, an sha biki, an bar masu luguden lebe da maganganu a kafar sada zumunta.
A wani labarin, kun ji yadda wani dattijo ya lallaba, ya yi wuf da wata ‘yar karamar yarinya ba tare da bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng