Ikon Allah: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar shekara 15 a Arewacin Najeriya (Hotuna)

Ikon Allah: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar shekara 15 a Arewacin Najeriya (Hotuna)

Toh fa, soyayya gamon jini ce amma idan da kauna, haka zalika hausawa na cewa soyayya ruwan zuma idan an sha a ba masoya, sai dai wasu lokuttan, idan aka duba irin soyayyar da wasu masoya ke yi, sai ya zamto kamar wata almara.

Hakan ya tabbata ne kamar yadda aka sha bikin wani Alhajin kauye mai shekaru saba’in da doriya a rayuwa, Alhaji Yakubu Chanji yayin daya auri wata yar karamar yarinya mai shekaru goma sha biyar a rayuwa, a jahar Neja.

KU KARANTA: Kwankwaso ya karbi sabbin mabiya daga masana’antar Kannywood

Ikon Allah: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar shekara 15 a Arewacin Najeriya (Hotuna)
Yakubu
Asali: UGC

Majiyar Legit.com ta ruwaito makwabtan angon sun bayyana cewar an daura wannan aurene a gidansu yarinyar dake garin Lapai na jahar Neja a ranar Litinin 10 ga watan Disamba, bikin daya samu halartar baki, yan uwa da abokan arziki.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, makwabtan Alhaji Canji sun tabbatar da cewa yana yawan aure kuma yana yawan saki, don haka auri-saki ne, wannan halayya tasa ce tasa ake masa lakabi da suna ‘Canji’ sakamakon yawan canza matan aure da yake yi.

Ikon Allah: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar shekara 15 a Arewacin Najeriya (Hotuna)
Yakubu
Asali: UGC

“Ana kiransa da Canji ne saboda yana yawan canza matan aure, a iya sani na yayi aure sau goma sha biyu, amma wasu da suka sanshi sosai sun ce sau ashirin yana auren mata.

“Abinda muka sani kawai shine yana ajiye mata hudu a gidansa a ko yaushe, da zarar ya saki guda daya, ko kuma ta mutu, zai auro wata sabuwa ba tare da bata lokaci ba.” Inji wani makwabcinsa.

A hannu guda kuma, makwabtan Alhaji Canji sun bayyana shi a matsayin mutum mai kyauta da taimako, musamman taimakon al’ummar unguwar Kwangila, inda suka ce ya bada gagarumar gudunmuwa wajen gina babban masallacin unguwar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng