Ina Son Gwamnati Mai Jiran Gado Ta Ci Gaba da Yaki da Rashawa Daga Inda Na Tsaya, Inji Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana rokonsa ga gwamnati mai zuwa, inda yace ya kamata a ci gaba da yaki da rashawa
- Shugaban ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta yi kokarin kafa tubalin lallasa ‘yan rashawa a duk inda suke a kasar ta Najeriya
- Sai dai, a baya shugaban ya amince da yiwa wasu tsoffin gwamnoni biyu afuwa duk da tabbatar da ‘yan rashawa a kotu har uku
FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana cewa, ya yi shimfidin yaki da rashawa mai dorewa a gwamnatinsa na shekara takwas mai karewa.
Shugaban ya kuma bayyana cewa, yana fatan gwamnati mai jiran gado za ta bi tafarkinsa na tabbatar da ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Channels Tv ta ruwaito.
Karin Bayani: Tinubu Ya Magantu Kan Gwamnatin Da Zai Kafa, Ya Yi Watsi Da Batun Gwamnatin Hadin Gwiwa
Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis a lokacin da ya gana da mahukuntan kotun da’ar ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta Danladi Umar a gidan gwamnati da ke Abuja.
Rashawa illa ce ga kowace kasa - Buhari
Ya bayyana cewa, rashawa babbar illa ce ga kowace kasa a duniya, inda ya yaba da kokarin da kotun yake yi wajen yakar rashawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakazalika, ya kuma yabawa shugaban tawagar da ta gana dashi da kuma sauran hukumomin yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Ya ce, sun tsaya tsayin daka don tabbatar da an fatattaki rashawa a Najeriya duk da kuwa babu wadatattun ma’aikata da kudaden gudanar da ayyukan, Daily Trust ta ruwaito.
Na kafa tubakin yaki da rashawa, inji Buhari
Da yake magana, Buhari ya ce:
“Fatanmu ne a ce tubalin da muka kafa a gwamnatin nan zai ci gaba da tafiya, kasancewar batun rashawa lamari ne da ke zama babbar barazana ga dukkan kasashe.”
Kafin hawansa mulki a Najeriya, daya daga cikin abubuwan da Buhari ya yiwa ‘yan Najeria alkawari akwai tabbatar da yaki da rashawa a kasar.
Gwamnatin Buhari ta yiwa tsoffin gwamnoni ‘yan rashawa afuwa daga dauresu da aka yi
Sai dai, a baya kun ji yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da yiwa tsoffin gwamnonin jihohin Taraba da Filato bayan da aka tabbatar da sun ci kudin kasa kuma an daure su a kotu.
Wannan lamarin ya haifar da cece-kuce a Najeriya, amma duk da haka aka sake su tare da wanke su daga laifin bisa umarnin manyan masu fada a ji a Najeriya.
Daya daga abin da ke ba gwamnatin Najeriya shine tabbatar da hukuncin kotu kan ayyukan rashawa da aka gudanar a kasar nan, musamman kan manyan ‘yan siyasa.
Asali: Legit.ng