An Sako Gwamna Dariye da Nyame da Buhari ya Yafewa daga Magarkama

An Sako Gwamna Dariye da Nyame da Buhari ya Yafewa daga Magarkama

  • Watanni bayan da shugaban kasa Muhammadu ya yiwa tsoffin gwamnonin Taraba da Filato afuwa, sun rabu da zaman gidan kasa
  • A yau ne muka samu labarin cewa, an sako tsoffin gwamnoni, kuma tuni aka ce sun samu ladartarwa a gidan gyaran hali
  • 'Yan Najeriya sun yi ta cece-kuce yayin da gwamnatin kasar nan ta ambata yafewa gwamnoni biyu da ake zargi da cin kudin kasa

FCT, Abuja - Yanzu muke samun labarin cewa, an sako tsoffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba, Sanata Joshua Dariye, da Jolly Nyame daga gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne watanni uku bayan afuwar da majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi musu a ranar 14 ga Afrilu, 2022.

Wata majiya daga gidan gyaran halin ta shaida wa jaridar Daily Trust, cewa an saki tsoffin gwamnonin ne da misalin karfe 2:15 na rana a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa fitaccen tsohon shugaban 'yan sandan Najeriya rasuwa

Afuwar Buhari: An sako Nyame da Dariye daga gidan gyaran hali
An Sako Gwamna Dariye da Nyame da Buhari ya Yafewa daga Magarkama | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Haka kuma an saki wasu fursunoni uku daga cibiyar gyaran hali ta Suleja a jihar Neja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar majiyar:

"An yi musu afuwa bisa rashin lafiya, yawan shekaru da kyawawan halaye da ladabtuwa da suka koya yayin da suke a cibiyar gyaran hali."

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, Abubakar Umar bai samu ba.

An yankewa Nyame zaman gidan yari na shekaru 12 ne bisa samunsa da laifin karkatar da Naira biliyan 1.64 a lokacin da yake gwamnan Taraba, yayin da Dariye kuma zai auna a gidan yari na shekaru 10 a kan zambar Naira biliyan 1.126.

Matakin da majalisar ta dauka na sakin gwamnonin biyu 'yan rashawa ya haifar da cece-kuce a Najeriya, ganin yadda shugaba Buhari ke yawan ambatan yaki da rashawa a matsayin abin da ya sa a gaba.

Kara karanta wannan

Hausawan Arewacin Najeriya na cikin zaman dar-dar a Imo yayin da IPOB suka kashe 'yan Nijar 8

A rahoton Vanguard, kakakin hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya na Abuja, Humphrey Chukwuedo, ya tabbatar da sakin gwamnonin biyu.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ba a sake su ba tun watan Afrilu, kakakin ya ce Hukumar ba za ta sake su kawai ba saboda furucin baki daga shugaban kasa.

Buhari ya yafewa Joshua Dariye, Jolly Nyame, da wasu fursunoni 157

A tun farko, majalisar kolin kasa (masu mulki da tsaffin shugabanni) ta yafewa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame da tsohon gwamnan Plateau, Joshua Dariye, dake garkame a kurkuku yanzu.

Gwamnonin biyu na cikin fursunoni 159 da majalisar ta yafewa ranar Alhamis karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Daga cikin wadanda aka yafewa tsohon soja da minista lokacin Abacha, Tajudeen Olanrewaju; Laftanan Kanar Akiyode, da dukkan Sojojin da aka daure kan laifi a hannu cikin yunkurin juyin mulkin Gideon Orkar a 1990.

Kara karanta wannan

Mulkin Buhari: Burodi ke kan gaba a jerin abincin da ke son fin karfin talakan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel