NDLEA Ta Aika Muhimmin Sako Ga Masu Neman Aikin da Hukumar Za Ta Dauka
- Hukumar nan ta NDLEA ta shirya daukar mutanen da suke sha’awar za su yi aiki da ita
- A ranar farko da aka bude shafin neman aikin, mutane kimanin 200, 000 suka yi ca a kansa
- NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta ce yanzu an shawo kan wannan matsala
Abuja - NDLEA mai yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta tabbatarwa masu neman aiki da ita cewa ana kokarin magance matsalolin da ake samu.
An bude kafar yanar gizo domin masu sha’awar aiki da hukumar NDLEA su nema, sai dai hakan ya zo dacikas kamar yadda aka tabbatar a makon nan.
Hukumar tarayyar ta fitar da sanarwa ta bakin Kakakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya ce ana magance matsalar da aka samu wajen neman aiki.
Da yake magana a ranar Laraba, Femi Babafemi ya ce tun a ranar Talatar nan hukumar ta bunkasa fasaharta ta yadda mutane 53, 170 suka nemi gurabe.
Jama'a sun yi yawa a shafin
Rahoton tashar talabijin na Channels ya ce an dauki matakin ne bayan mutane sun yi wa shafin yawa a ranar Lahadi da aka fara shirin daukar aikin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A lokaci guda aka samu sama da mutane fiye da 200, 000 da suke neman yadda za su shiga shafin.
Babafemi a madadin hukumar NDLEA ya nemi afuwar wadanda suka yi yunkurin neman aikin ba tare da nasara ba, ya ce an kawo karshen matsalar a yanzu.
Sanarwar da aka fitar a makon nan, ta kara da kira ga masu sha’awar aiki da hukumar su yi hakuri yayin da ake kokarin juye bayanai a uwar garken.
Menene yake jawo haka?
Mun tattauna da Malam Ibrahim Dattijo Makama wanda masani ne a harkar IT kuma kwararre a ilmin PHP domin jin abin da yake jawo matsalar.
Ibrahim Dattijo Makama ya shaida mana cewa wasu shafukan Najeriya ba su da karfin da za su iya karbar adadin masu ziyara da-dama a lokaci daya.
Masanin ya ce kamar titi ne maras fadi ya cika da motoci, har ta kai abin hawa sun fara bi ta gefen hanya, idan cinkoso ya yi yawa, sai ayi carko-carko.
Siyasar addini da kabilanci
Idan aka shiga fannin siyasa, za a ji labari Femi Gbajabiamila ya na cewa da yawa daga cikin abokan aikinsa a zauren majalisa sun sha kashi a zaben da ya gabata.
Shugaban majalisar ya ce mutane ba su duba irin kokarin wakilansu a majalisar tarayya ko kuwa aikinsu a mazabunsu ba, an fi la’akari da addini da kabilanci.
Asali: Legit.ng