Abin da Ya Jawowa Jiga-jigan ‘Yan Majalisa Rasa Kujerunsu a Bana – Gbajabiamila
- Femi Gbajabiamila bai ji dadin sakamakon zaben 2023 ba, yana ganin majalisar tarayya tayi rashi
- Shugaban majalisar wakilan tarayyan kasar ya zargi masu zabe da amfani da addini da kabilanci
- Gbajabiamila yana ganin ba a duba alheri da cigaban da ‘yan majalisa ke kawowa a mazabunsa ba
Abuja - Femi Gbajabiamila ya koka a kan yadda siyasar shekarar nan ta 2023 tayi aman dadaddun ‘yan majalisar da ake ji da su a mazabun tarayya.
A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto Rt. Hon. Femi Gbajabiamila yana cewa an yi amfani da addini da bangaranci a zaben 25 ga watan Fubrairun 2023.
Shugaban majalisar wakilan tarayyan ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa makonni bayan an shirya zaben.
Gbajabiamila ya ce ba ayi la’akari da irin kokarin ‘yan majalisar a zaben bana ba, abubuwan da suka yi tasiri a guguwar su ne addini da kabilanci.
"Wasu ba su yi sa'a ba" - Gbaja
“An sha gumurzu, ba ni kadai ba, har da da yawa daga cikin abokan aikinmu a zauren majalisar nan. Dukkanmu 360, wasu sun yi sa’a, wasu ba su yi ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ina cewa sa’a saboda zaben bai zo yadda ya kamata ba, ba a duba irin kokarin ‘yan majalisar a zauren majalisar tarayya ko kuwa a mazabunsu ba.
Sai dai aka duba wasu abubuwa da-dama dabam. Batun addini ne. Batun kabilanci. Ina sa ran mu cigaba, zabe ya zaba an yi la’akari da kokari.
- Rt. Hon. Femi Gbajabiamila
P/Times ta rahoto Hon. Gbajabiamila yana cewa dalilin kawo dokar zabe kenan saboda a kawo gyara a kasa.
‘Dan siyasar yake cewa ya yi bakin kokarinsa na ganin an rika yin amfani da kato da kato wajen tsaida ‘dan takara kafin jam’iyya ta shiga babban zabe.
A cewar Gbajabiamila, a zaben tsaida gwani wasu ‘yan majalisar suka rasa damar zarcewa a kujerunsu, da aka shiga babban zabe aka barar da wasu.
Abin da ya faru a zaben nan ba zai taimakawa siyasar Najeriya ba a ra’ayin na uku a kasar.
Nasarar Rufai Hanga
Rahoto ya zo cewa Rufai Hanga ya kafa tarihin zama mutum na farko da ya wakilci Kano ta tsakiya sau biyu a majalisar dattawa, INEC ta ba shi shaida.
Duk da shugaban INEC ya ce ba zai canza Ibrahim Shekarau, a karshe Hanga ya yi nasara a kotu, ya yi abin da tsofaffin gwamnoni biyu ba su iya yi ba.
Asali: Legit.ng