Atiku da PDP Sun Janye Sabuwar Karar da Suka Shigar Na Beman Duba Kayan Aikin Zaben Na INEC
- Wani lamari mai daukar hankali ya faru a Najeriya game da zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Faburairu
- Rahoton da ke shigowa a yau ya bayyana cewa, jam’iyyar PDP da dan takarar sun janye daga karar da suka shigar kan INEC
- A baya, Atiku da PDP sun bayyana shiga kotu don ba su damar bincika takardun aikin zaben shugaban kasa da aka yi
FCT, Abuja – Jam’iyyar PDP da kuma dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar sun janye daga karar da suka shigar kan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).
PDP da Atiku sun shigar da kara a baya don ba su damar bincike ga takardun da aka yi amfani dasu wajen zaben shugaban kasa.
A cewar wani rahoton Tribune Online, lauyan Atiku da PDP ya shaidawa kotun daukaka kara cewa, ba sa bukatar ci gaba da neman abin da suka gabatar.
Tawagar lauyoyin karkashin jagorancin Joel-Kyari Gadzama ta ce tuni ta mika takardar janyewa daga batun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin da yasa aka janye batun
Game da dalilin janye batun, lauyoyin sun ce, hukumar zabe ta tunkari PDP da lauyoyinta game da batun tuntuni.
Hakazalika, lauyoyin sun ce a wata ganawa da INEC ta yi da lauyoyin PDP da Atiku, an warware zare da abawa kan abubuwan da ake bukata game da kayan aikin zaben.
A bangarensa, mai shari’a Joseph Ikyegh ya amince da bukatar tare da tabbatar da cire karar daga jerin abin da za a duba, rahoton Vanguard.
Idan baku manta ba, ‘yan takarar shugaban kasa na Labour da PDP sun ce za su shigar da karar kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2023.
Kasar Amurka ta taya Tinubu murnar lashe zabe, sun tura sako ga ‘yanb Najeriya
A wani labarin, kun ji yadda kasar Amurka ta ba ‘yan Najeriya shawarin cewa, su yi hakuri da fitowar Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na bana.
Hakazalika, kasar ta taya Tinubu murnar lashe zabe, inda tace an yi aiki daidai da tsarin dimokradiyya, kamar yadda rahoto ya bayyana.
Kasar ta yi kira ga a kwantar da hankali, kana ta tabbatar da cewa ta fahimci akwai abubuwan da suka faru da yawa a zaben na bana.
Asali: Legit.ng