Tawagar Lauyoyin Jam’iyyar Labour Sun Gana da INEC Kan Yiwa Kayan Zabe Kwakwaf
- Tawagar lauyoyin Peter Obi sun shiga ganawa da hukumar zabe mai zaman kanta a babban birnin tarayya Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ya basu damar bincike kan kayan aikin zaben bana na shugaban kasa
- A baya, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi ya bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa na bana
FCT, Abuja - Tawagar lauyoyin jam’iyyar Labour ta su Peter Obi ta gana da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) game da batun bincika kayan aikin zaben bana, Vanguard ta ruwaito.
Shugaban tawagar lauyoyin Labour, Dr. Livy Uzookwu ne ya jagoranci sauran lauyoyi 60 a ganawarsu da hukumar INEC.
Ana kyautata zaton zai yi bayani ga manema labarai bayan ganawar ta kammala, wacce ake yi a hedkwatar INEC da ke Abuja.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton dai ba a bayyana abubuwan da wadannan lauyoyin suka tattauna da hukumar zabe ta INEC ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda zaben shugaban kasa ya kasance
An yi zabe a ranar 25 ga watan Faburairu, inda aka alanta Bola Ahmad Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zabe, Punch ta ruwaito.
‘Yan takarar jam’iyyun PDP da Labour sun ce ba za su amince ba, don haka suka tunkari kotu don ba su damar bincika kayan aikin zaben.
Bayan zuwa kotu, Peter Obi da Atiku Abubakar sun nemi kotun ya basu damar yin duba ga kayayyakin da aka yi amfani dasu a zaben na bana.
Daga nan ne kotun daukaka karan ya ce, su yi duba tare da yin kwafin takardun da suka cancanta don iya kafa hujja a gaban kotun da za su daukaka kara.
Da Zafi-Zafi: Jam'iyyar Labour Ta Yi Barazanar Mamaye Ofisoshin INEC Na Kasa Baki Daya, Ta Bayyana Dalili
Ba wannan ne karon farko da ake kalubalantar zaben shugaban kasa ba a Najeriya, an sha yin hakan a baya.
Ba Tinubu bane zabin Allah, inji Peter Obi
A wani labarin kuma, kunji yadda Peter Obi ya yiwa Aisha Buhari martani game da batun cewa, Tinubu ne Allah ya zaba ya mulki Najeriya.
A cewarsa, bai kamata a kawo batun Allah ne ya zabo Tinubu ba, saboda an yi murdiya a zaben bana.
Daga nan ya bayyana cewa, bai amince da sakamakon zaben na bana ba, kuma zai tafi inda za a kwata masa hakkinsa.
Asali: Legit.ng