‘Obi ne gwarzo ba’: Wike ya ce Peter Obi ya haramtawa Arewa ci gaba da mulki, ya fadi dalili
- Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana yadda Peter Obi ya haramtawa Arewa kujerar shugabancin kasar nan
- A cewar Wike, da Peter Obi bai fito takara ba, Atiku ne zai kwashe kuri’un mutanen yankin Kudancin kasar nan
- Wike da wasu gwamnoni biyar a Najeriya na PDP sun bayyana rashin amincewarsu ga tafiyar dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar
Fatakwal, jihar Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ne gwarzonsa a zaben da aka yi na shugaban kasa.
A cewar Wike, bayyanar Obi da karfi a zaben bana ne ya haramtawa ‘yan Arewa ci gaba da mulkar Najeriya daga inda Buhari ya tsaya, The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya yi maganganu ne masu daukar hankali game da siyasar kasar nan a ranar Asabar a birnin Fatakwal, jihar Ribas.
Peter Obi nake goyon baya a boye
A cewar Wike, sabanin yadda ake yada cewa bai goyi bayan Obi ba, mutane sun gaza gane cewa, Obi ne ma gwarzonsa a zaben na bana, Channels Tv ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewarsa:
“Obi ne gwarzo na. Idan da Obi bai yi takara ba, da mulki zai sake komawa Arewa. Ilahirin yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da PDP ta rasa, idan Obi bai yi takara ba da PDP ne za ta ci.
“Gwarzon wananan zaben dai Obi ne ko kuna so ko baku so. Ban zo nan don na faranta muku ba, Obi ne gwarzon. Ta yiwu ba a alanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba, amma babu matsala, doka za ta yi aikinta."
Wike ya ce, dalilin da yasa bai fito karara ya bayyana dan takarar da yake goyon baya ba saboda gwamnonin G5 sun amince da samar da shugaban kasa ne daga Kudu don ya gaji Buhari.
Bayan lashe zabe, Tinubu zai gana da zababbun ‘yan majalisun Najeriya
A wani labarin kuma, kunji yadda jam’iyyar APC ke fafutukar nemawa Tinubu abokan aiki a mulki kuma masu fahimta iri daya.
A wannan yunkurin, Tinubu zai gana da ‘yan majalisun da aka zaba a zaben bana saboda tattauwa batutuwa masu yawa.
Ana kyautata zaton za su tattauna kan batun da ya shafi zaban shugabannin majalisar dattawa da kuma majalisar wakilai ta kasa.
Asali: Legit.ng