An Hallaka Mutane da Yawa Yayin Da ’Yan Banga Da ’Yan Bindiga Suka Ba Hammata Iska a Katsina
- Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun hallaka mutane da yawa a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
- Rahoto ya bayyana yadda tsagerun suka yi dauki ba dadi da ‘yan bangan sa kai a wani yankin jihar ta Katsina
- Ana ci gaba da fuskantar tashin hankali daga hare-haren ‘yan ta’adda a yankuna daban-daban na Najeriya
Jihar Katsina - Ana fargabar ‘yan kauye da yawa sun mutu wasu da yawa kuma sun jikkata a ranar Asabar yayin wata fada da ta barke tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a yankin Kankara na jihar Katsina.
A cewar majiya mai karfi daga yankin, ‘yan ta’addan suna kan hanyarsu ta halartar taron bikin wani shugabansu ne da ake kira ‘Mai Katifa Mutuwa’ lokacin da suka gamu da ‘yan bangan, rahoton Vanguard.
Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da ke yawan gamuwa da matsalar hare-haren ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin Najeriya.
Yadda lamarin ya faru
Majiya ta ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Tsakanin karfe 3 zuwa 4 jiya, mun gano cewa wasu ‘yan banga sun yi kicibus da wasu ‘yan bindigan da suka zo kauyen Majifa don halartar bikin daya daga cikin shugabanninsu da aka fi sani da ‘Katifa Mutuwa.’
“Rikicin da suka yi ya kai ga an farmaki wasu kauyukan da ke kusa a yankin yayin da ‘yan bindigan suka yi ta harbin kai mai uwa da wabi.
A cewar majiyar, sun kashe mutane sun kai biyar a Gurbi da kuma wasu 13 da aka samu an kashe a tsakanin Majifa, Makera da Gidan Jifau.
Kauyukan da aka farmaka
Hakazalika, majiyar ta ce, ‘yan bindigan sun mamaye kauyuka 10 a yankin da suka hada da Gurbi, Danmarke, Majifa, Gidan Baso, Gidan Sarka, Gidan Jiho, Gidan Ancho, Gidan Sanka, Dan mangoro, Gidan Sale da dai sauransu.
Ya zuwa daren jiya, an gano gawarwakin mutum 18 da aka kashe da kuma wasu mutum 15 da aka jikkata, inda aka kai su asibitin kwararru na Kankara.
A cewarsa, daya daga cikin wadanda aka kwantar a asibitin na Kankara ya rasu bayan wani dan lokaci.
'Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da kirga mutanen da suke ta mutuwa a wannan mummunan lamari.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar fadan, amma ya ce har yanzu akwai kura a bayanan faruwar lamarin.
Ya dai yi alkawarin sanar da manema labarai halin da ake ciki bayan samun bayanai wadatattu daga sauran hukumomin tsaron da suka kai dauki a harin.
A irin wannan yanayi a Kduna aka tsinci gawarwakin mutane 10 da 'yan bindiga suka kashe babu gaira babu dalili.
Asali: Legit.ng