CBN Ya Rufe Shirin Musanya Tsohon Kuɗi da Sabbi a Kauyukan Najeriya

CBN Ya Rufe Shirin Musanya Tsohon Kuɗi da Sabbi a Kauyukan Najeriya

  • Duk da kuɗi ba su yawaita hannun yan Najeriya ba, CBN ya dakatar da shirin musayar sabbin naira a karkara
  • Mai magana da yawun babban bankin, Isa Abdulmumin, ya ce dama sabon shirin ba na dindindin bane yana da lokaci
  • Kungiyar masu POS ta ce sabon shirin bai kai yadda aka yi tsammani ba saboda wasu dalilai

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya ce damar da mutanen karkara suka samu na sauya tsohon kuɗinsu a basu sabbi ta hanyar shirin musaya ta ƙare.

Muƙaddashin mai magana da yawun CBN na ƙasa, Isa Abdulmumin, ne ya bayyana haka yayin hira da wakilin jaridar Punch ta wayar tarho.

Sabbin naira.
CBN Ya Rufe Shirin Musanya Tsohon Kuɗi da Sabbi a Kauyukan Najeriya Hoto: CBN
Asali: UGC

A kalamansa ya ce:

"An dakatar da shirin musaya, dama CBN bai kawo shirin don ya zauna dindindin ba, yana da lokacin da aka ɗibar masa."

Kara karanta wannan

"Na rantse da Allah ban taba ɗaukar sisin Jihar Kaduna ba, wanda ya Ƙaryata Yazo Mu Dafa Kur'ani" - El-Rufai

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kungiyar wakilan bankuna da masu POS ta bayyana cewa shrin bai amfanar da komai ba, inda ta jaddada cewa ba'a jawo masu ruwa da tsaki ba yayin aiwatar da tsarin.

Me shirin musayar kuɗin CBN ya ƙunsa?

CBN ya ce ya bullo da tsarin musaya ne domin baiwa mutanen ƙauye da masu rayuwa a yankunan da babu rassan banki damar sauya tsohon kuɗinsu da sabbin naira da aka canja.

Domin baiwa kowa dama bai ɗaya, CBN ya cire masu Mobile Money da POS a Abuja da Legas, ya jaddada cewa shirin musayan na kowa ne ko da baka da Asusun banki.

Babban bankin ya ce kowane mutum ɗaya zai iya musanya N10,000 ne kacal a tsarin musaya.

Shirin bai amfanar da komai ba - AMMBAN

Amma Jami'il hulda da jama'a na AMMBAN ta ƙasa, Oluwasegun Elegbade, ya ce da shirin musayan kuɗin CBN ya yi abinda a ka yi tsammani da bankuna basu sha fama da harin fusatattun 'yan Najeriya ba.

Kara karanta wannan

"Ku yafe min dan Allah": Inji Direban Motan da Yayi Kicibis da Jirgin Ƙasa a Lagos Mutum 6 Suka Mutu

"Shirin bai taka rawar da aka yi tsammani ba, da a ce ya yi aiki yadda ya kamata, da ba za'a samu rikice-rikice kan karancin naira a faɗin ƙasa ba."
"Mun yi tsammanin za'a ɗauki mutane da yawa, amma sai aka bar masu aikin su yi yadda suka ga dama ba tare da an sa musu ido yadda ya kamata ba. Ba tare da sa ido ba, da yawan jihohi sun yi son ransu."

A wani labarin kuma Gwamna Ya Yi Watsi da Buhari da CBN, Ya Tsawaita Wa'adin Amfani da Tsohon Naira a Jiharsa

Gwamnatin Bayelsa ta raba gari da jawabin Buhari kan tsohon kuɗi, ta ce tsohon N200, N500 da N1000 zasu ci gaba da amfani kamar yadda Kotun koli ta ce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel