Babban Sarkin Mai Addinin Gargajiya Ya Fada Wa Tinubu Abin Da Zai Yi Wa 'Yan Adawa

Babban Sarkin Mai Addinin Gargajiya Ya Fada Wa Tinubu Abin Da Zai Yi Wa 'Yan Adawa

  • Oba Adetoyese Olakisan, shugaban Ogboni Aborigine Worldwide ya shawarci Asiwaju Bola Tinubu kada ya yi ramuwar gayya ga yan adawa
  • Sarkin mai addinin gargajiya ya ba wa tsohon gwamnan na Legas wannan shawarar ne cikin wata budaddiyar wasika da ya fitar a ranar Laraba
  • Oba Olakisan ya fada wa Tinubu cewa Allah ya riga ya zabe shi a matsayin uban kasa, don haka ya mayar da hankali wurin gyaran kasa da hada kan yarbawa

An bukaci zababben shugaban kasa, Sanata Bola Tinubu, kada ya yi ramuwar gayya ga wadanda ba su goyi bayansa yayin neman zama shugaban kasa ba, rahoton The Punch.

Shugaban Ogboni Aborigine Worldwide, Oba Adetoyese Olakisan, ne ya bada shawarar a wata budaddiyar wasika da ya aika wa Tinubu kwafi da aka samu a Osogbo a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Dage Da Addu'a Don Kawai Allah Ya Ba Tinubu Nasara, Gwamnan APC Ya Magantu

Sarki da Tinubu
Sarkin yarbawa ya shawarci Tinubu ya yafe wa yan adawa. Hoto: Oluaye Oba Ogboni Agbaye Adetoyese Abdul Olakisan/The Nation
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Olakisan, wanda ya bukaci shugaban kasar mai jiran gado ya yi aiki tukuru don ceto kasar daga mawuyacin halin rayuwa, ya ce Allah ne ya mayar da Tinubu matsayin uban dukkan yan Najeriya.

Ya kuma ce hadin kan al'ummar Yarbawa ya danganta kan Tinubu, ya kuma shawarce shi ya yi aiki don sauya tsarin roban arzikin kasa a Najeriya.

Wani sashi na wasikar ta ce:

"Kada ka manta ba za ka rayu har abada ba. Aikin ka na da lokaci. Aikin ceto za ka yi. Ka yi aiki tukuru kamar rana daya ka ke da shi, amma ka yi shiri tamkar shekara takwas ka ke da shi.
"Kada ka yi ramuwar gayya. Allah ya shige maka gaba kuma ka yi nasara, don haka wane za ka yaka kuma? Allah ya mayar da kai uban dukkan yan Najeriya. Ka dauki duk wadanda suka kawo maka matsala a matsayin sanadin nasararka.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

"Kana iya kyautatawa ta hanyar sake tsarin rabon kasa. Ka jajirce kan tsarin tarayya na ainihi tun zamanin NADECO. Ka san abin da na ke fada kuma Allah zai taimake ka. Yi aiki don sake fasalin Najeriya."

Hadin Kan Yarbawa Ya Dogara Da Kai

"Hadin kan al'ummar Yarbawa ya dogara kan ka. Kungiyar Afenifere da wasu kungiyoyin biyu sun zama karnuka marasa hakora, ba su da alkibla ga yarbawa, ba wani jajirtaccen shugaba kuma. Asiwaju, kai mai canja lamura ne, ka mayar da yarbawa matsayinsu na jagoranci."

Atiku ya ziyarci IBB a gidansa da ke Minna

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu ya ziyarci Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa ziyarar ta Atiku ba za ta rasa alaka da zaben da aka kammala ba inda ya Bola Tinubu ya zama zababben shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164