NRC Ta Yi Karin Bayani Kan Abinda Ya Jawo Karon Jirgin Kasa da Mota a Legas

NRC Ta Yi Karin Bayani Kan Abinda Ya Jawo Karon Jirgin Kasa da Mota a Legas

  • Hukumar sufurin jiragen kasa ta yi karin haske kan abinda ya haddasa haɗari tsakanin Jirgin ƙasa da Motar Bas a Legas
  • Daraktan NRC (MD), Fidet Okhiria, ya ce lokacin da Direban zai tsallake layin dogon duk motoci sun tsaya jirgi ya wuce
  • Ya ce bai san meyasa Direban ya ci gaba da tafiya ba amma ya kamata matafiya su rika kula da wurare irin waɗan nan

Lagos - Daraktan Hukumar Sufurin jiragen kasa (NRC), Mista Fidet Okhiria, ya yi bayani kan wanda ya haddasa haɗarin jirgin ƙasa da Motar Bas a jihar Legas da safiyar Alhamis.

Daily Trust ta rahoto cewa jirgin ƙasan NRC ya murkushe motar Bas din mai ɗauke da ma'aikatan gwamnatin jihar Legas yayin da zai wuce ta Layin dogo da ke yankin Sogule.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin Ƙasa Yayi Taho Mu Gama Da Wata Mota a Legas, Fasinjoji Da Dama Sun Jikkata

Hadarin jirgin kasa a Legas.
Yadda jirgin kasa ya murkushe motar Bas a Legas Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Kawo yanzu bayanai sun nuna cewa an zakulo gawar mutane uku daga cikin fasinjojin motar yayin da wasu da dama suka ji raunuka.

Wanene ya jawo hatsarin?

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN), Okhiria ya ce:

"Bayanan da na tattara a wurin da hatsarin ya faru sun nuna cewa da yawan motoci sun tsaya jiran Jirgin ya wuce amma Direban motar ma'aikatan gwamnatin ya ci gaba da tafiya, ban san meyasa ba."
"Mai yuwuwa Diraban ya yi tunanin zai wuce inda Layin dogon ya ratsa ne kafin Jirgin kasan ya kariso kusa, amma hakan ba ta yuwu ba, shiyasa jirgin ya murƙushe motar Bas din, iya bayanan da muka samu kenan."
"Jirgin kasan ya taso ne daga Ijoko zuwa Iddo."

MD, wanda ya nuna tsantsar damuwarsa da halin da ma'aikatan gwamnatin Legas suka tsinci kansu, ya roki matafiya su ƙara kula sosai idan zasu tsallake layin dogo.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an Tsaro Wuta, Da Yawa Sun Mutu a Kaduna

Mista Okhiria ya ƙara da cewa a duk lokacin da Motoci zasu tsallake wuri irin haka, bai kamata su manta da wurin da aka yi alamar tsayawa ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

“Wasu Na Shirin Haddasa Rikici Bayan Zaben Gwamnoni”, DSS Ta Gargadi Yan Najeriya

A wani labarin kuma DSS ta bankado wani shiri na haddasa tashin tashina bayan zaben gwamnoni da yan Majalisun jihohi.

Jami'an tsaron farin kaya ta ce wasu 'yan siyasa na shirin kitsa tashin hankali bisa haka ta gargaɗi matasa su guje wa duk wani abu da zai kawo rikici bayan zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel