Za a Kai Wani Makon a Haka – ‘Yan Kasuwa Sun Yi Magana Kan Wahalar Fetur
- Watakila sai bayan zaben Gwamnonin jihohi sannan man fetur zai samu sosai a jihohin da ke Arewa
- ‘Yan kasuwa sun shiga dar-dar bayan zabe, saboda haka aka daina zuwa dauko fetur a yankin Kudu
- Idan aka kammala zabukan bana ba tare da wani rikici ba, motoci za su cigaba da yin jigilar man fetur
Abuja - Babu mamaki wahalar man fetur za ta cigaba a garin Abuja da sauran jihohin Arewacin Najeriya har zuwa bayan zaben Gwamnonin jihohi.
A ranar Talata ne Punch ta rahoto ‘yan kasuwa su na cewa akwai yiwuwar man fetur ba zai samu ba, ganin yadda layi suka kara tsawo a gidajen mai.
Mutanen garuruwan Abuja, Nasarawa, Neja da kuma wasu jihohin Arewa sun koma gidan jiya a makon nan, samun fetur ya yi kamari a yankunan.
Rahoton ya ce a wasu gidajen man, abin ya kai ana saida litar fetur a kan N400. ‘Yan bumburutu kuwa su na saida litarsu a tsakanin N450 zuwa N500.
Matsalar 'Yan bumburutu
Matsalar da mutane suke fuskanta ita ce masu bumburutu sun fi ganewa a ba su tsabar kudi, a lokacin da kusan kowa ya koma cefane ta yanar gizo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Ya ‘yan kungiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu da ke harkar mai a Najeriya, sun tabbatar da cewa 90% na gidajen mansu a rufe suke a halin yanzu.
Abin da ya jawo hakan kuwa ba komai ba ne illa karancin kaya. A daidaikun gidajen da ake iya samun man, akwai ‘dan karen tsada da kuma dogon layi.
A gidajen man Conoil da Total da suke kusa da hedikwatar kamfanin NNPC a birnin Abuja, sai an ci karo da matsanancin layi kafin a iya sayen man fetur.
Abin da ya jawo hakan - IPMAN
Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ya shaidawa jaridar cewa da alama wahalar man da ake yi zai shiga mako mai zuwa.
Abubakar Maigandi ya ce jama’a sun yi tunanin za ayi rikici bayan zabe, saboda haka sai suka daina jigilar fetur a jihohinsu, hakan ya sa mai ya yi karanci.
Idan dai har babu rigimar da ta barke, zuwa mako mai zuwa za a iya ganin mai ya samu sosai.
Shugabannin IPMAN su na sa ran motocinsu su shiga Legas domin dauko mai muddin aka kammala zaben Gwamnoni ba tare da fada ya kaure ba.
INEC ta fasa shirya zabe
Mun samu labari cewa da alama har Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai da masaniyar cewa Shugaban Hukumar INEC zai daga zaben jihohi a jiya.
Daga dawowa daga kasar waje, jirgin Shugaban Najeriyan ya sauka a Katsina da shirin yin zabe, kwatsam sai ga sanar cewa an daga zaben Gwamnoni.
Asali: Legit.ng