Afenifere Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Dan Takarar Da Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023
- A karshe Afenifere ta bayyana dan takarar shugaban kasa da ya lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023
- A sabuwar sanarwa, kungiyar hadin kan Yarbawar ta dage cewa Mr Peter Obi ne ya lashe zaben shugaban kasar
- Yayin da ta ke watsi da nasarar dan takarar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kungiyar ta bukaci Obi ya kallubalanci sakamakon zaben a kotu
Kungiyar hadin kan Yarbawa ta Afenifere, ta dage cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Mr Peter Obi ne ya lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ba dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress, APC ba, Bola Tinubu.
A ranar Talata, 7 ga watan Maris na 2023, Afenifere ta ce tana goyon bayan matakin da Obi ya dauka na kallubalantar sakamakon zaben shugaban kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Afenifere ta dage Peter Obi ne ya lashe zaben
Hakan na cikin wani sakon bayan taro ne da kungiyar ta fitar bayan babban taronta na musamman, da aka yi a Isanya-Ogbo, jihar Ogun, a ranar Talata, wani rahoto da Vanguard ta fitar ya tabbatar.
"Babban taron, da kakarfar murya ya yi watsi tare da raba Afenifere daga duk wani sakon taya murna da sunan kungiyar ko kowanne dan takara da INEC ta sanar ba bisa ka'ida ba."
Sabon matsala ga Tinubu, INEC A Yayin Da Peter Obi Ya Shigar Da Sabuwar Kara a Kotu
Mr Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour a zaben shugaban kasa da aka kammala a baya-bayan nan ya shigar da sabuwar kara na neman a bashi damar bincika na'urar BVAS da aka yi amfani da su yayin zaben.
An shigar da karar mai lamba CA/PEC/09m/23 ne a kotun daukaka kara da ke birnin tarayya, Abuja a ranar Laraba 8 ga watan Maris na shekarar 2023.
A karar, Obi da jam'iyyar Labour suna neman kotun ba basu damar bincika na'urar tantance masu zabe, BVAS, da sauran kayan zabe masu muhimmanci da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta yi amfani da su.
PDP ta ki amincewa da nasarar Tinubu na APC, ta ce Atiku ne ya lashe zabe
Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta soki ayyana Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe da INEC a yi.
Jam'iyyar ta PDP din ta dage cewa dan takararta, Atiku Abubakar shine ya lashe zaben shugaban kasar.
Asali: Legit.ng