Kotun Koli Ya Tabbatar da Lawal a Matsayin Dan Takarar Gwamna Na PDP a Jihar Zamfara

Kotun Koli Ya Tabbatar da Lawal a Matsayin Dan Takarar Gwamna Na PDP a Jihar Zamfara

  • Kotun koli ya bayyana cewa, ya amince da zabo Dauda Lawal Dare a matsayin dan takarar gwamnan Zamfara na PDP
  • An kai ruwa rana a kotu har guda uku a Najeriya kan batun sahihin dan takarar gwamnan Zamfara na PDP
  • Sau kwanaki hudu zaben gwamna a Najeriya, ana ci gaba da shiri kamar yadda aka yi na shugaban kasa

FCT, Abuja - Kotun kolin Najeriya ya tabbatar da Dauda Lawal a matsayin sahihin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, rahoton Channels Tv.

Tabbatarwar na zuwa ne kwanaki hudu gabanin zaben gwamna da za a yi a Najeriya a ranar 11 ga watan Maris kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta tsara.

Kotun daukaka kara mai zamansa a jihar Sokoto a ranar 6 ga watan Janairu ya yi watsi da hukuncin kotun tarayya da ya kori Dauda a matsayin dan takarar da zaben fidda gwanin PDP a Zamfara ya samar.

Kara karanta wannan

Tsohon Ministan Buhari da Tsohon Gwamna Su na Hangen Shugabancin Majalisar Dattawa

Hukuncn kotun koli kan sahihin dan takarar gwamna na PDP a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda batun ya soma

An kalubalanci zaben fidda gwanin ne a kotun tarayya da ke zama a Gusau, babban birnin Zamfara, inda alkali ya umarci a sake yin sabon zaben na fidda gwani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An sake zaben a ranar 23 ga watan Satumba, kuma har ila yau Dauda ne ya sake lashewa, duk da haka aka sake rusa zaben saboda wasu dalilai, Leadership ta ruwaito.

Basu amince da hukuncin kotun tarayya ba, Dauda Lawal-Dare, shugaban kwamitin zaben fidda gwanin PDP, Adamu Maina Waziri da Bala Mande sun tunkari kotun daukaka kara.

Wadanda ake kara

Wadanda ake kara sun hada Dr Ibrahim Shehu-gusau, Alhaji Wadatau Madawaki, Hafiz Nahuche da hukumar hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

A hukuncin da mai shari’a Abubakar Talba ya yanke a madadin sauran alkalan kotun kolin, ya ce masu shigar da karan sun cike dukkan ka’idoji, don haka kotu ya yi hukunci daidai da bukatarsu.

Kara karanta wannan

Muje zuwa: Sanata ya fadi wulakacin da gwamnan CBN zai gani bayan saukar Buhari

Dan takarar Labour ya koma APC, ya hada kai da Binani

A wani labarin kuma, kunji yadda dan takarar LP na gwamna a Adamawa ya bayyana hada kai da ‘yar takarar gwamna ta APC a jihar.

A cewarsa, zai hada kai da ita ne saboda suna da ra’ayoyi iri daya masu kyau da ka iya kai wa ga ci gaban jihar.

Ana ci gaba da shirye-shirye don tunkarar zaben gwamna a Najeriya nan da ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.