Yadda ’Yan Najeriya Ke Cikin Kuncin Takardun Kudi Duk da Umarnin Kotu Na Ci Gaba da Kashe Tsoffin Naira
- Bayan hukuncin kotun koli kan batun ci gaba da kashe tsoffin Naira, har yanzu 'yan Najeriya na cikin matsi
- Bincike ya nuna har yanzu ba a fara karbar tsoffin kudaden ba, kuma gwamnati bata yi magana a kai ba
- An daina kashe tsoffin kudi N500 da N1000 tun ranar 10 ga watan Faburairu, lamarin da ya jawo cece-kuce
‘Yan Najeriya na ci gaba da dandana kudarsu game da karancin kudi duk kuwa da hukuncin da kotul koli ya yanke na ci gaba da kashe tsoffin Naira.
A makon da ya gabata, kotun koli ya ce a ci gaba da kashe tsoffin N200, N500 da N1000 har zuwa karshen watan Disamban bana.
Bincike ya nuna cewa, har yanzu ‘yan Najeriya, musamman ‘yan kasuwa da direbobi da ma masu gidajen mai ba sa karbar tsoffin kudaden kasancewar CBN ya ce sun daina amfani tun 10 ga watan Faburairu.
A bangare guda, wani darakta a CBN ya ce, babban bankin zai ba da umarni ga bankunan kasuwanci kan yadda hukuncin na kotun koli zai shafe su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, babban bankin zai zauna da masu ruwa da tsaki tare da yanke shawari kan yadda za a bullo wa batun kotun na koli.
Jaridar Daily Trust ta yi kokarin jin ta bakin daraktan yada labarai na CBN, Isa Abdulmumini amma abin ya ci tura, domin bai amsa waya ba, kuma bai dawo da sakon tes da aka masa ba.
Meye abin da gwamnatin Buhari ta ce?
Yayin da aka tuntubi hadimin shugaban kasa, Femi Adesina kan batun, ya ce a tuntubi ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami.
Amma Malami da hadiminsa na yada labarai, Umar Gwandu duk basu amsa kiran waya ba kuma basu dawo da sakon tes da aka tura musu ba.
Sai dai, wani babban lauya a ofishin ministan da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa, gwamnati za ta bi umarnin kotun.
A cewarsa:
“Babu yadda za a yi a ce mai girma atoni-janar zai ce gwamnati ba za ta bi umarnin kotun koli ba; ba ma zai faru ba.
“Ku jira zuwa ranar Litinin, ina da tabbacin zai yi magana.”
Halin da ‘yan kasuwa ke ciki
Tattaunawa da ‘yan kasuwa a bangarori da yawa a kasar na nuni da cewa, har yanzu suna zaman dar-dar din karbar tsoffin kudaden.
Wani dan kasuwa a Kantin Kwari da ke jihar Kano, Adamu Hamza ya ce, duk da ‘yan kasuwa na fuskantar matsi kan wannan sabuwar doka, amma ba za su ci gaba da karbar kudin haka siddan ba.
A cewarsa, suna tsoron kada su karba daga baya kuma su rasa inda za su ke kai kudaden.
Wani kuma, Yakubu Muhammad ya ce ‘yan kasuwan na jiran abin da CBN za ta ce ne kafin su ci gaba da karbar kudaden.
Ya ce:
“Ba za mu yi kasadar ba. Muna gani a kullum, ba a girmama shari’ar ma a yanzu ko kadan.”
Haka nan a jihar Kaduna, bincike ya nuna masu ababen hawa da direbobin motoci ba sa karbar tsoffin kudaden duk da umarnin kotu.
Haka nan, bata sauya zani ba a jihohin Ribas, Ondo da Legas, gidajen mai da cibiyoyin kasuwanci da yawa ba sa karbar tsoffin N500 da N1000.
Gidan mai da tashar mota a Gombe ba sa karbar tsoffin kudi
A ziyarar wakilin Legit.ng Hausa a gidan mai na Jiri Brothers da ke Hammadu-Kafi a jihar Gombe, a nan ma ba a karbar tsoffin kudade, kana ba sa ba da canji ga wanda ya biya kudi ta POS.
A cewar daya daga cikin ma’aikatan gidan man:
“Gaskiya ba ma karbar tsoffin kudi saboda mai gidan man ya ce kada mu karba. Kuma ya ce kada mu ba da canji na ‘cash’ wa duk wanda ya sayi mai ya nemi a ba shi canji.
“Wani zai ce ka cire N1000 amma a saka masa man N800 a bashi canjin N200, an hana mu yin hakan.”
Muhammad Abubakar Isa, wani fasinja da zai tafi Kano daga tashar motar Dukku ya bayyana kokensa ga yadda ya sha wahalar biyan kudi ta hanyar tiransfa a tashar kasancewar babu sabbin kudi, tsoffin kuma ba a karbarsu.
A bangare guda, Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bi umarnin kotun don sassautawa ‘yan kasa.
Asali: Legit.ng