Jami’ar ABU Ta Kera Nau’ikan Motoci 3 Masu Daukar Hankali, Har da Mai Aiki da Ruwa
- Jami’ar ABU da ke Zaria ta yi abin a yaba, ta kera mota mai amfani da ruwa a matsayin makamashi ba fetur ba
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke kokarin fuskantar matsalar makashin fetur saboda karancinsa
- Ya zuwa yanzu, jami’ar ta ce akwai bukatar hada karfi da karfe tsakanin gwamnati, masana’antu da kuma jami’o’i
Zaria, jihar Kaduna - Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria ya ce, nan ba da jimawa za ta kera mota ‘yar Najeriya kuma mai amfani da ruwa a madadin fetur.
Wannan na fitowa ne daga bakin shugaban tsangayar injiniyanci na jami’ar, Farfesa Ibrahim Dabo a ranar Asabar 4 ga watan Maris yayin da bikin ranar injiniyanci ta duniya da aka yi.
Dabo ya bayyana cewa, akwai hobbasa da da yawa jami’ar ta ABU ke yi, ciki har da kera mota mai amfani da wutar lantarki da kuma motoci mai saukaka dumamar yanayi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya kara da cewa, tsangayar tasa na aiki tukuru wajen kera motar da zata sauya akalar tuki da hawa motoci, ta hanyar amfani da ruwa a matsayin makamashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Motar tsere da bata shan man fetur da yawa
Ya kuma shaida cewa, daya daga cikin motocin da ake aiki kai, za ta iya tafiyar kili-mita 100 ba tare da kone man fetur da ya wuce lita 1 tak ba.
Hakazalika, ya ce tuni an kai motar kasar Afrika ta Kudu, kuma tabbas ta yi aiki daidai yadda ake abukata.
Har ila yau, ya ce jami’ar na aiki don ganin ta sake rage yawan amfani da man fetur a motar da ake kera.
Sai dai, ya ce motar da ya kira ‘shell eco-marathon’ na daukar mutum biyu ne kacal, kuma an yi ta ne don yin wasannin tseren motoci.
Kalubalen da ake samu, da kira ga gwamnati
A bangare guda, ya ce motar da aka kera mai amfani da wutar lantarki kuwa na daukar mutum hudu karkarinta.
Dabo ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ya karfafa gwiwar abin da jami’o’in kasar ke samarwa na ci gaba don habakawa da bunkasa kira a nan cikin gida Najeriya.
Ya kuma yi kira ga hadin gwiwa tsakanin makarantu da kuma masana’antu a fadin kasar, People’s Gazette ta tattaro.
Ya koka da cewa, da yawan masana’antun da ke zagaye da jami’o’in kasar nan a rufe suke, kadan ne ke aiki saboda karancin kayan aiki.
Ba wannan ne karon farko da ake kera abubuwa masu kyau ba a Najeriya, an kera jirgi mai saukar ungulu a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng