Hukumar NAFDAC ta samu sabon Shugaba a Najeriya
- An nada sabon Shugaba Hukumar NAFDAC na kasa
- Mai magana da bakin Hukumar kasar ya bayyana haka
- Shekarun tsohuwar Shugabar sun isa ajiye aiki a Najeriya
A jiya mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon Shugaban Hukumar NAFDAC mai kula da harkar maganguna da abinci na rikon kwarya.
An nada wani sabon Shugaban Hukumar NAFDAC na kasa ne bayan da shekarun tsohuwar Shugabar Yetunde Oni su ka cika 60 a watan jiya. Mai magana da bakin Hukumar kasar Dr. Abubakar Jimoh ya bayyanawa manema labarai na kasa watau NAN.
KU KARANTA: Diyar Shugaban kasa Buhari tayi wani korafi
Jimoh ya bayyana cewa Mista Ademola Magbojuri wanda yake ofishin Hukumar da ke Garin Kaduna kuma babban Darekta na Hukumar a yanzu ne zai ja ragamar Hukumar kafin a nada takamamen Shugaba.
An dai ta samun rikici a Hukumar saboda rashin biyan wasu alawus din Ma'aikata a daidai lokacin sa tsohuwar Shugaban ya zo karshe kwanaki.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Fayose zai kara da Shugaba Buhari
Asali: Legit.ng