Kada Ka Kuskura Ka Haɗa Gwamnatin Haɗaka Inji Tanko Yakasai Ga Tinubu
- Gwamnatin Haɗaka Wata Irin Gwamnati Ce Ta Haɗin Kan Ƙasa dake ƙunshe Da Duk Wata Jam'iyyar Ƙasa.
- Jim kaɗan Bayan Ayyana shi a matsayin wanda yayi Nasarar Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa, Wasu Masu Faɗa Aji Nata Bada Shawarar Ya Kafa Gwamnatin Haɗin Gwiwa Kawai
- Tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi Shima Ya Goyi Bayan Wannan Kira A Ranar Larabar Data Gabata
Mazan jiya a fagen siyasa da suka ga jiyan da yau suna da tasiri wajen bada shawarwari ga masu mulki.
Watakila hakan bai rasa nasaba da yadda suka goge tare da sanin yadda al'amuran mulki ke faruwa.
Sananne ɗan siyasar nan Alhaji Tanko Yakasai wanda yake daya daga cikin waɗanda suka kafa Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya gargadi zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu akan kada ya bada kai bori yahau akan buƙatar da wasu suke ƙoƙarin sako masa na kafa gwamnatin haɗaka.
Ita dai gwamnatin haɗaka wata irin gwamnati ce ta haɗin kan ƙasa dake ƙunshe da duk wata jam'iyya ƙasa (ko kuma manyan jam'iyyu), wanda ake haɗawa lokacin yaƙi ko kuma lokacin dokar taɓaci.
Dattijon mai faɗa aji, yayi gargaɗin ne a yayin gudanar da wata tattaunawa a gidan sa dake Abuja, ranar larabar data gabata.
Tinubu ya samu gagarumin rinjaye ne da ƙuri'u 8,794,726a APC, Atiku Abubakar kuma ya samu kuri'a 6,984,520 a PDP sai Peter Obi da yake da Ƙuri'u 6,101,533 a LP.
Sa'o'i kaɗan bayan bayyana tsohon gwamnan na Legos a matsayin sabon ango Najeriya, wasu masu hasashe da sharhi na bada shawarar ya kafa gwamnatin haɗin gwiwa kawai.
Sun bada uzurin yin hakan ne, saboda rage raɗaɗin fushi da ake fama dashi daga ƴan adawa da zaɓen ya haifar.
Tsohon gwamnan Ekiti, kuma tsohon shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi shima ya goyi bayan wannan kira a ranar larabar data gabata.
Amma Yakasai bai goyi bayan taba, inda yace ba abar so nace ga mulkin demokradiyya a kowacce irin al'umma.
Jaridar Punch ta ruwaito shi yana cewa:
" A'a, Gaskiya bazan bashi shawara yayi wata gwamnatin haɗin gwiwa ba. So nake Demokradiyya ta ta bunƙasa. Soke adawa a cikin demokradiyya, kashe demokradiyya ne A ƙyale kowa yazo da tsarin sa.
Tanko Yakasai ya ci gaba da cewa:
"Kuma ai masu kaɗa kuri'a ne suka zaɓe sa. Ya aiwatar da abinda yazo dashi. Abinda ya aiwatar idan ya gama, wani sai yazo ya ya gina daga inda ya tsaya. A haka ƙasa take cigaba. Kuma a haka gidan da muke zaune a ciki aka gina shi. Ayi fandisho, sai ayi gangar jiki, ayi plaster, azo ayi fenti da sauran su. Haka demokradiyya take a zahirance. Kuma haka yakamata ta kasance. Kuma haka mutanen ƙasashen duniya suke yi, saboda haka abin da Yakamata mu dinga yi kenan." Inji shi.
Zaɓukan 2023: Tinubu ya Aikawa Atiku da Obi Ƙwaƙwƙwaran Saƙo Bayan INEC Ta Ayyana Shi a Matsayin Mai Nasara
Masari Ya Shiga Sallamar Masu Rike da Mukamai Tun da Aka Kunyata Tinubu a Katsina
Rahotanni daga Katsina nunawa suke Gwamna Aminu Bello Masari ya soma garambawul a gwamnatinsa biyo Bayan shigo da Hon. Sani Ɗanlami cikin majalisar zartarwa a Katsina
Sannan ya naɗa Hon. Sani Ɗanlami ya zama Kwamishinan wasanni da matasa a madadin Bishir Gambo Saulawa
Sanarwar SSG ta ce shi kuma Bishir Saulawa ya koma ma’aikatar sifayo bayan cire Usman Nadada
Majiyar mu ta ce ana tunanin wadannan mutane sun yi wa APC zagon kasa a zaben da ya gabata.
Asali: Legit.ng