Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a Borno da Kuri’u 252,282
- Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Borno da ke Arewa maso gabas a Najeriya
- Ya samu kuri'u, inda ya ba abokin hamayyarsa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar kuri'u kusan 60,000 a zaben
- Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da tattara sakamakon zabe a Najeriya, Tinubu ya fadi a jiharsa ta Legas a Kudu maso Yamma
Jihar Borno - Dan takarar shugaban kasa a APC, Asiwajo Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasa a jihar Borno dake Arewa maso Gabashin Najeriya.
Rahoton da Legit.ng Hausa ta samu da jaridar Punch na cewa, dan takarar ya samu nasara ne a kananan hukumomi 27 na jihar .
Tinubu ya samu kuri'u 252,282, kamar yadda baturiyar zabe na jihar a zaben bana, Farfesa Jude Rabo ta sanar.

Asali: Facebook
Kananan hukumomin da Tinubu ya lashe
Kananan hukumonin da Tinubu ya lashe sun hada da Gubio, Kaga, Magumeri, Mafa, Kwaya Kusar, Konduga, Nganzai, Dikwa, Bayo, Abadan, Mobbar da Gwoza
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, shi ya samu nasara a Shani, Kala/Balge, Ngala, Marte, Jere, Askira, Chibok, Monguno, Damboa, Hawul, Guzamala, Biu da Kukawa.
Tinubu na ba dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar kusan kuri’u 60,000 a jihar, inda Atiku ya samu kuri’u 190,921, rahoton The Nation.
Peter Obi ya fi Kwankwaso farin jini a Borno
Peter Obi na jam’iyyar Labour ya samu kuri’u 7,205, inda Rabiu Kwankwaso na jam’iyyar NNPP mai kayan marmari ya samu kuri’u 4,626.
Jihar Borno ita ce jihar da abokin takarar Bola Ahmad Tinubu ya fito, kuma ana kyautata zaton yana da tasiri a siyasar yankin.
Kashim Shettima, abokin takarar Tinubu ya yi gwamna a jihar Borno, inda ya mikawa Babagana Umara Zulum mulki a zaben 2019.
Tinubu ya fadi a Legas
A wani labarin kuma, kun ji yadda Bola Ahmad Tinubu ya fadi a jiharsa ta Legas, Kudu maso Yammacin Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar Labour, Peter Obi ne ya fi kowa samun kuri'u a zaben jihar.
Atiku ne ya zo na uku a zaben, duk da cewa bai samu kuri'un da suka taka kara suka karya ba.
Asali: Legit.ng